1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarwarin zaman lafiya kan Sri Lanka ya ci tura.

October 30, 2006
https://p.dw.com/p/Bue2

A birnin Geneva, an tashi daga shawarwarin zaman lafiyar da aka shafe yini biyu ana yi, don sasanta rikicin ƙasar Sri Lanka, ba tare da cim ma wata madafa ba. Rahotanni sun ce, taron ya wargaje ne bayan da ɓangarorin gwamnati da na ’yan tawayen ƙasar, suka gaza cim ma daidaito kan tsai da ranar ci gaba shawarwarin. Babban mai shiga tsakani, Erik Solheim na ƙasar Norway, ya faɗa wa maneman labarai a birnin Genevan cewa, ɓangarorin biyu sun ki yarjewa kan batutuwan da suka shafi tsarin kai taimakon agaji ga jama’ar da yaƙin basasan ƙasar ke addabarsu. Amma duk da haka, sun yi alkawarin kiyaye ƙa’idodjin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cim ma qa cikin ashekara ta 2002.

Su dai ’yan ƙungiar Tamil Taigers, sun dage ne kan samun taimakon agaji ga ɗimbin yawan ’yan ƙabilar Tamil ɗin da yaƙin baya-bayan nan ya shafa, sa’annan kuma da neman a buɗe babban titin da ya haɗa makurɗaɗar Jaffna da sauran ƙasar.