1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawo kan rigingimu a nahiyar Afirka

October 23, 2010

Afirka Ta Kudu ta zargi Majalisar dinkin Duniya da nuna halin ko oho ga rikice rikicen da ke faruwa a yankin Afirka

https://p.dw.com/p/Pm2E
Zauren taron kwamitin sulhun Majalisar Dinkin DuniyaHoto: cc-by-sa-Patrick Gruban

Kasar Afiurka Ta Kudu ta zargi kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da yin hanzari wajen shawo kan rigingimun da suka kunno kai a wasu yankunan da ba na Afirka ba, sabanin yadda ta ke tinkarar na Afirka, inda kasar ta bukaci kwamitin ya kara yin namijin kokari wajen agazawa ayyukan wanzar da zaman lafiya a nahiyar. Batun gaza warware yakin da aka dade ana gwabzawa a kasar Somalia ne yasa kasar ta Afirka Ta Kudu ta baki jakadanta a majalisar Baso Sanguqu tayar da batun a wajen muhawarar da kwamitin sulhun ke yi, inda Afirka ta ce rundunar ta dake Somalia tana fuskantar matsalolin kudi a kullu yaumin, kana majalisar ba ta baiwa dakarun kulawar da ta dace.

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU tana da dakarun wanzar da zaman lafiyar da yawan su yakai dubu bakwai da 500 a kasar Somalia, wadanda ke tallafawa gwamnatin wucin gadin kasar, amma kuma dakarun na samun kudin daya gaza wanda dakarun wanzar da zaman lafiyar Majalisar Dinkin Duniya ke samu a sauran wurare. Galibin dakarun dai sun fito ne daga kasashen Uganda da Burundi.

Jakadan kasar Afirka Ta Kudu a Majalisar Dinkin Duniya Baso Sanguqu ya shaidawa kwamitin sulhun cewar, kasashen Afirka sun dauki matakin tura dakarun wanzar da zaman ladiya a wuraren da majalisar ko dai ta nuna halin ko oho ko kuma ba ta dauki wani mataki ba. Da ya ke tsokaci game da rikicin Somalia da kuma yankin Darfur, Jakadan ya ce 'yan Afirka da dama na da ra'ayin cewar, kwamitin sulhun zai dauki mataki ne kawai bayan an yi ta kissar wadanda basu ji ba basu gani ba tare da zubar da jinin su, gabannin watakila kwamitin ya sauke nauyin dake kansa na bada kariya da kuma samar da zaman lafiya a nahiyar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala