1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara 10 bayan kisan kiyashin birnin Srebrenica

Mohammad Nasiru AwalJuly 11, 2005

A yau aka cika shekara 10 da kisan kiyashin da sojojin Sabiyawan Bosniya suka yiwa al´umar Musulmin Srebrenica

https://p.dw.com/p/Bvas
Musulmin Bosniya a makabartar wadanda aka yiwa kisan kiyashi a 1995
Musulmin Bosniya a makabartar wadanda aka yiwa kisan kiyashi a 1995Hoto: AP

A lokacin da ya kama aiki a matsayin kwamandan dakarun MDD a Srebrenica cikin watan maris na shekarar 1993, janar Phillipe Morillon dan kasar Faransa ya tabbatarwa al´umar birnin cewa ka da su damu domin daga wannan lokaci suna karkashin kariyar MDD. A lokacin sanyin hunturun wannan shekara mutane kimanin dubu 40 ke wannan birni, wato ´yan asalin birnin da kuma ´yan gudun hijira da suka tsere daga ta´asar sojojin Sabiyawan Bosniya.

A shekarar ta 1993 kwamitin sulhu na MDD ya mayar da birnin Serbrenica karkashin ikonsa, kana kuma an kwance damarun kusan dukkan sojojin rundunar Bosniya da Herzegovina sannan aka girke dakarun MDD.

To amma watanni kalilan bayan haka sai birnin ya fada cikin wani bala´i, inda sojojin Sabiya suke hana ayarin motocin MDD dauke da kayan taimako shiga birnin, yayin da cinikin kayan abinci ta bayan fage ya zama ruwan dare sannan a shekarar 1995 birnin ya tsunduma cikin halin matsananciyar yunwa.

A cikin watan yunin wannan shekara sojojin Sabiyawan Bosniya sun yiwa birnin kofar rago kana suka yi ta kaiwa sansanonin dakarun MDD farmaki, abin da ya yi sanadiyar janyewar sojoji kasar NL daga yankin da sojojin MDD ke gadi. A ranar 6 ga watan na yuni aka kaddamar da wani farmaki akan birnin inda aka fara akan yankin dake karkashin kariyar dakarun MDD. Janar Ratko Mladic ne kuwa ya ba da umarnin kai wannan hari kamar yadda aka saurara ta wayar sadarwa ta hannu.

O-Ton Mladic: Schießt nur auf die Lebanden…

„Ku yi harbi akan masu rai kawai, akan masu rai kawai ba sa dauke da makami, kananan bindigogi ne kawai garesu.“

A lokacin an ki jin kiran da Holland ta yi na kungiyar tsaro ta NATO ta ba da taimako kana kuma ta kai farmaki ta sama, bisa hujjar cewa Maldic bai da niyar mamaye birnin. Sai a ranar 11 ga watan yuli NATO ta kai wani kwarkwaryar farmaki da bai haifar da da mai ido ba. A wannan rana ce kuwa wakilin MDD na musamman Yasushi Akashi ya ba da sanarwar cewa birnin Serbrenica da kuma sansanin sojin kasar NL sun fada hannun dakarun Sabiya.

Kimanin kashi 2 cikin 3 na mutane dubu 40 a birnin na Serbrenica sun tsere zuwa sansanin MDD dake Potocari da fatan samun kariya daga dakarun MDD. Yayin da wasu mutane dubu 10 daukacinsu maza suka bi cikin daji don shiga garin Tuzla. Wadanda suka nemi mafaka a Potocari sun zargi dakarun NL da mikasu ga abokan gabarsu, wadanda a da ma ke shirin yi musu kisan gilla.

Tun daga wannan lokaci ne kuwa sojojin Sabiya suka rika yiwa musulmin Bosniya da suka kama kisan kiyashi a boye da kuma a bainar jama´a. Sannan suna binnesu a manyan ramuka don boye shaidar aikata wannan ta´asa.

Wasu hotuna da jiragen saman Amirka masu bincken ainihin abin da ya faru suka dauka, ya nunar da cewa akwai irin wadannan ramuka sama da 40, inda aka binne sama da mutane dubu 7 ciki har da mata da kananan yara da aka yiwa kisan gilla.