1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara 5 bayan harin ƙunan bakin waken ran 11 ga watan Satumba ta 2001.

YAHAYA AHMEDSeptember 4, 2006

A cikin wannan watan ne za a cika sherau 5 da kai harin ƙunan baƙin waken nan na ran 11 ga watan Satumba a biranen New York da Washington a Amirka. To ko wane hali ake ciki a duniya yanzu, bayan ƙaddamad da yaƙi da ta'addanci da Amirka ta yi tun wannan lokacin?

https://p.dw.com/p/BtyN
Harin ƙunan baƙin waken ran 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 a birnin New York
Harin ƙunan baƙin waken ran 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 a birnin New YorkHoto: AP

A ganin ’yan siyasa da dama dai, harin ƙunan bakin waken ran 11 ga watan Satumban shekara ta 2001, wato wani muhimmin dandali ne na tarihi. Wato wannan ranar, ta canza ababa da dama a duniya. Babu shakka kuma, yayata ɓarnar da harin ya janyo da ɗimbin yawan jama’an da suka rasa rayukansu da gidajen talabijin suka dinga yi, ta ƙara baƙanta wa Amirkawa ransu. A ko yaushe dai, tun wannan lokacin, shugaba Bush ba ya ɓata lokaci wajen nanata wa duk wanda ke sauraronsa cewa Amirka ta sami kanta cikin yaƙi.

Ba a taɓa dai samun wani lokaci a tarihi ba, inda Amirka ta fi kutsawa cikin ƙasashen musulmi kamar a wannan karon. Ta hakan ne dai ta hamɓarad da gwamnatin Taliban a Afghanistan, saboda ita ce take zargi da bai wa ƙungiyar al-Qaeda mafaka da maɓuya, wajen tsara shirye-shiryen kai wannan harin na ran 11 ga watan Satumba. Har ila yau kuma, Amirka da abokan burminta na ƙasashen Yamma, a cikinsu kuwa har da Jamus, na da ɗimbin yawan dakaru girke a Afghanistan ɗin. Bayan haka kuma, Amirkan na katsalandan a wasu ƙasashen musulmin, wai don bunƙasa tafarkin dimokraɗiyya. Amma musulmi da dama na ganin hakan ne tamkar ƙaddamad da yaki a kansu. Ba sa kuma yin amanna da wannan tafarkin na halin rayuwar ƙasashen Yamma. Wato a ganinsu, keɓe addini daga harkokin mulkin ƙasa, kamar yadda dimukraɗiyya ta tanada, bai dace da tafarkin addinin islaman ba. Bugu da ƙari kuma, sai ga shi Amirkan ce muhimmiyar abokiyar burmin Isra’ila a yankin Gabas Ta Tsakiyar. Duk waɗannan al’amuran dai sun mai da Amirkan abokiyar gaba a mafi yawan ƙasashen musulmi. Sabili da haka ne kuwa, duk wanda ya buga ƙirji, ya ƙaddamad da yaƙi kann Amirkan, kamar dai Usama Bin Laden, yake samun cikakken goyon bayan jama’a da dama a duniyar musulmin.

Harin ƙunar baƙin waken ran 11 ga watan Satumban da ake zargin Bin Laden da kaiwa, shi ne farin wata ambaliyar hare-hare da tashe-tashen hankulla, wadda ke ta ƙara yaɗuwa a duniya. A ɗaya ɓangaren ma, za a iya lura da cewa, ba waɗanda ’yan ta’addan ke kira kafurai ne tahse-tashen hankullan suka fi addaba ba. Kusan kashi 90 cikin ɗari na waɗanda suka rasa rayukansu ko kuma suka zamo naƙasassu, sakamakon hare-haren ta’addancin, musulmi ne. Za a fi iya tabbatad da hakan ne a Iraqi, inda mabiya ɗariƙun shi’itti da na ahlili sunna ke yaƙan juna, ko kuma inda masu tsatsaurar ra’ayin islama ke yaƙan masu sassaucin ra’ayi.

Tun cikin shekarun1990 ne dai Bin Laden ya ƙaddamad da yaƙi kan abin da ya kira “gamayyar masu yaɗa aƙidar Yahudanci“. Manufofin da ya sanya a gaba dai sun sha bamban da na tafarkin haɗayyar tattalin arzikin duniya, alal misali. Mai yiwuwa harin ƙunan baƙin waƙen ran 11 ga watan Satumba ma, wani yunƙuri ne na bayyana adawa ga manufofin da ƙasashen Yamma suka sanya a gaba, kuma suke son angaza wa sauran duniya su. Sai dai tarihi na nuna cewa, duk wani yunƙurin nuna adawa ga ci gaban al’ummomi, a ƙarshe yana cin tura. Duk kuma mai ƙoƙarin ƙaryata shirin tausaya wa bil’Adama, bai taɓa samun nasara ba. Aƙidar Nazi dai na nuna misali a zahiri. Duk da cewa dai Usama Bin Laden ya sami maɓuya ne a kan iyakar Afghanistan da Pakistan, amma har ila yau, angizonsa na samun yaɗuwa a kusan ko’ina a duniya.

Babu shakka, za a daɗe ana wannan gwagwarmayar, tsakanin ƙasashen Yamma da waɗanda suke kira ’yan ta’adda.