1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SHEKARA DAYA BAYAN FADADA KUNGIYAR EU: MASU FARA'A DA DA MASU KUKA.

YAHAYA AHMEDApril 28, 2005

A ran 1 ga watan Mayun shekarar bara ne aka yi bikin karbar sabbin kasashe 10 cikin Kungiyar Hadin Kan Turai. Hakan kuwa ya sa yawan al’umman duk kasashen kungiyar ya habaka da mutum miliyan 75.

https://p.dw.com/p/BvcE
Ofishin taron Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai a birnin Brussels.
Ofishin taron Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai a birnin Brussels.Hoto: AP

A halin yanzu dai kungiyar, mai mambobi 25, na da yawan al’umma miliyan dari 4 da 55. Ko me shiga cikin kungiyar ya janyo wa sabbin kasashen, bayan shekara daya da zamowarsu mambobi ? Su kuma tsoffin kasashe mambobin, wane irin kalubale suka huskanta a cikin wannan lokacin ?

A ran 1 ga watan Mayu ne Kungiyar Hadin Kan Turai, za ta yi bikin cika shekara daya da fadada iyakokinta zuwa wasu yankunan gabashi da kudancin nahiyar, inda kasashe 10 suka shigo cikin kungiyar, suka zamo cikakkun mambobi bisa manufa. Wani binciken da aka gudanar dai na nuna cewa, sabbin kasashen kungiyar, sun gamsu da shekarar da ta wuce a matsayinsu na mambointa. Sun ga bunkasar tattalin arzikinsu, suna kuma samun tallafi daga kungiyar EUn. Matasa da yawa ne ke amfani da damar da suka samu ta yin tafiye-tafiye ba tare da huskantar shingen binckensu a kan iyakoki ba. Da yawa daga cikinsu kuma sun yi amfani da shirin nan na musayar dalibai, don fadada iliminsu a jami’o’in wasu kasashen kungiyar da suka zaba da kansu.

A tsoffin kasashe mambobin kungiyar kuwa, ba haka lamarin yake ba. Mazauna wadannan kasashen, musamman ma a yammacin Turai, sun fi nuna damuwarsu ne da fadada kungiyar da aka yi. Saboda suna ganin cewa, kwararowar ma’aikata daga kasashen gabashin Turai, wata barazana ce ga guraban aikinsu. Su dai `yan sabbin kasashe mambobin kungiyar, a shirye suke su yi aiki da samun albashi maras tsoka. A cikin wannan halin ne kuwa da yawa daga cikinsu ke aiki a masana’antar sarrafa motocin nan ta Volvo a kasar Sweden.

Wasu kasashe kamar Faransa da Jamus dai na adawa da salon da Sweden ke bi. Sun fi son a kayyade albashi mafi kankanta ne da za a dinga biyan ko wane ma’aikaci, a duk kasashen kungiyar. Hakan dai, a nasu ganin, zai rage yawan kauran da matasa ke yi daga yankunan gabashin Turai zuwa yamma don neman aiki. Idan ko ba a yi haka ba, ma’aikata, musamman ma dai masu sana’ar hannu, na fargabar rasa wuraren aikinsu ne a kasashen Yamman.

A fannin noma ma, manoman kasashen yammacin Turan na ta kara bayyana fargabarsu ta cewa, shigowar kayayyakin albarkatun noma daga sabbin kasashen zai karya darajar kayayyakinsu a kasuwa. A halin yanzu dai, ran al’umman kasashen yammacin Turai a tashe yake sosai da wannan sabon hali da aka shiga ciki. Gwamnatin Faransa ce kuma ta fi damuwa matuka, saboda zaben raba gardamar da za a gudanar a kasar a cikin watan gobe, kan amincewa ko kuma yin watsi da sabon kundin tsarin mulkin kungiyar EUn da aka riga aka gabatar. Binciken jin ra’ayin jama’a dai na nuna cewa, mafi yawan al’umman Faransan ne ke adawa da sabon kundin.

A daura da wasu kasashen yammacin Turan dai, kasar Birtaniya, ba ta nuna rashin jituwarta da shigowar ma’aikata daga kasashen kungiyar ba.

Sharadin da ta shimfida musu ne kawai, yin rajista da hukuma idan sun shigo kasar. Ta hakan ne kuwa, gwamnatin Birtaniyan ke iya sa ido kan hada-hadar da ake yi a kasuwar kwadago, take kuma iya karbar haraji.

A cikin kasashen gabashin Turan dai, `yan kasar Hungary ne suka fi zama gida, ko kuma idan sun fita ma, sun fi zuwa kasar Austriya ne, wato makawbciyarsu.

A kasashen yankin Batik kuma, wato Estoniya, da Litueniya, da Latviya, tattalin arzikinsu tun da suka shigo cikin kungiyar EUn, sai bunkasa yake yi.

Kasashen kudancin nahiyar, wato Malta da Cyprus, su kadai ne kasashe kuma tsibirai na bahar Rum da ke cikin kungiyar. A nan ma ana iya ganin farfadowar tattalin arzikinsu, tun da suka shiga cikin kungiyar. Sai dai ita Cyprus har ila yau na huskantar matsalar siyasa. Kasar a rabe take har yanzu. Kudancin tsibirin ne ke cikin kungiyar EU. Arewacinsa kuma, wanda mazaunansa Tukawa ne, ba ya cikin kungiyar. To wannan rabuwar ne dai har ila yau ke janyo wa kasar cikas a wasu bangarorin.