1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara daya bayan rasuwar Malam Yassir Arafat

Ibrahim saniNovember 11, 2005

Har yanzu ana jika a kokarin da ake na warware rikicin dake tsakanin israela da yankin palasdinawa

https://p.dw.com/p/Bu4H
Hoto: AP

Ya zuwa yanzu dai rahotanni da suka iso mana daga yankin na Palasdinawa na nuni da cewa dubbannin mutanen yankin ne suka yi tururuwa izuwa Muqataa,fadar marigayin don jinjina masa bisa irin namijin kokarin da yayi a lokacin yana raye wajen ganin yankin ya samu yantacciyar kasa mai cin gashin kanta.

Kafin dai hakan sai da Shugaban kasar yankin wato Mahmud Abbas da Faraminista Ahmed Qorei suka aza harsashin wani katafaren gini a yankin na Ramallah da zai kunshi masallaci da kuma gurin ajiye kayan tarihi, wanda idan an kammala shi za´a sa masa Sunan marigayi Arafat don kara nuna girmamawa a gareshi da kuma tunawa dashi.

Mahmud Abbas, wanda aka zabe shi a matsayin gurbin Malam Yassir Arafat na shugaban Palasdinawa yayi alkawarin watan wata rana sai an mayar da gini irin wanda aka dasa danbar sa a yankin na Ramallah izuwa Jaruselem inda Malam Yassir Arafat yayi fatan a binne shi idan ya rasu a lokacin yana raye.

Idan dai za a iya tunawa gwamnatin Israela ta hana a binne marigayin a wannan yanki dake birnin na Jerusselem bisa hujjar cewa Jerusselem a cikin kasar israela take.

Marigayi Abu Ammar,wanda ijiniya ne na gine gine,ya fara wannan gwagwarmayar ne a tun lokacin yana dalibi a can kasar masar,daga baya kuma ya koma izuwa Kuwait,a inda a wannan lokacin ne ya zamo mamba a cikin kungiyyar PLO mai fafutikar yanto Palasdinu,wanda daga baya kuma ya zamo shugaban ta na gaba daya.

Wani abin mamaki a cewar masu nazarin siyasa na kasa da kasa shine duk da rasuwar marigayi Yassir Arafat, alummar Palasdinawa naci gaba da kallon hotunan sa a matsayin kwarin gwiwa a garesu naci gaba da fafutikar neman yantacciyar kasar su, wanda a bakin wannan aikin ne Allah yayi wa Abu Amar,wanda akafi sani da suna Yassir Arafat Rasuwa.

A lokacin da shugaban kasar wato Mahmud Abbas yake jawabi a gaban dubbin mutanen da suka hallara a yankin na Ramallah, ya kara jaddada matakin da gwamnatin sa ta dauka naci gaba daga inda Malam yassir arafat ya tsaya game da gwagwarmayar da yayi na ganin an samu Yantacciyar kasa ta Palasdinu wacce keda hedikwatar ta a Birnin Jerusselem a lokacin yana raye.

Bugu da kari Mahmud abbas ya kara da cewa dole ne aci gaba da wannan gwqagwarmaya musanmamma bisa irin sadaukar da kann da Yassir Arafat yayi a lokacin yana raye don ceto Palasdinawa daga kangin da suke ciki.

A waje daya kuma duk da wannan kallo na gwarzon namiji da Palasdinu kewa Arafat, Mahukuntan israela da Amurka na kallon sane a matsayin mutumin dake kawo tsaiko dangane da kokarin da akeyi na tabbatuwar zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, musammamma a tsakanin yankin Palasdinawa da kasar Israela.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa shekara daya bayan rasuwar Arafat, babu wani ci gaba na azo a gani da aka samu game da kokarin da ake na sasanta rikicin dake tsakanin kasar ta israela da kuma yankin na Palasdinawa.

Za a iya gane hakan ne kuwa bisa irin tashe tashen hankula da rikice rikice da ake fama dasu bisa hare haren rokoki da kunar bakin wake, sannan a daya hannun kuma ga irin kutsaen da sojojin israela kewa Palasdinawa a wasu garuruwan dake yankin.

Bayan watanni goma sha biyu da rasuwar Arafat, har yanzu likitoci sun gaza gano wani abu da zai tabbatar da cewa anyi amfani da guba ne wajen kashe malam Yassir Arafat, mutumin daya taba samun kyautar hadin gwiwa ta zaman lafiya tare da Yitzhak Rabin tsohon Faraministan Israela a shekara ta 1994.