1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara daya da gabatar da shari'a akan Saddam Hussein

October 19, 2006

Shekara daya bayan gabatar da shari'a akan tsofon shugaban Iraki ba wani ci gaban da aka samu bisa manufa

https://p.dw.com/p/Btxg
Saddam Hussein
Saddam HusseinHoto: AP

“Ka san ni. Ka san kowane ne ni tun da kai dan kasar Iraki ne. Ba zan amsa wata tambaya daga wannan kutu ta jeki na yi ki ba. Mamayar da aka yi bata a bisa ka’ida kuma ina so a bani cikakken hakki na a matsayina na halastaccen shugaban kasar Iraki.”

Wannan bayanin an ji shi ne daga bakin tsofon shugaban kasar Iraki Saddam Hussein lokacin da alkalin dake shugabantar zaman shari’arsa ya nemi da ya gabatar da kansa. Hakan kuwa ya faru ne a daidai ranar 19 ga watan oktoban bara lokacin da aka gabatar da zaman farko na shari’ar tsofon shugaban na kasar Iraki. Ganin cewar ana nuna zaman shari’ar kai tsaye ta gidajen telebijin a sassa daban-daban na duniya, Saddam Hussein bai yi wata-wata ba wajen neman yin amfani da wannan dama domin yunkurin nuna wa duniyar cewa har yau shi ne ke rike da ragamar shugabancin kasar ta Iraki. Bayan da aka karanta masa ire-iren laifukan da ake zarginsa da wasu mukarrabansa su bakwai da aikatawa, abin da ya hada da kisan gillar da aka yi wa wasu ‘yan shi’a 148 a garin Dujail, nan take Saddam ya kakkabe kansa daga wannan laifi, daidai da abin da lauyoyinsa suka fada masa.

“Duka-duka abin da shugaban kasa yayi a game da matsalar Dujail shi ne yayi biyayya da abin da daftarin tsarin mulkin kasa ya tanadar masa inda ya rattaba hannu akan takardar hukuncin kisa da alkali ya yanke. Shi ma shugaba George Bush, a matsayinsa na gwamnan jihar Texas sai da ya albarkaci hukunce-hukunce na kisa kimanin 152.”

Zaman shari’ar na farko ba dore ba, inda bayan sa’o’i 3 kacal aka dage zaman zuwa 28 ga watan nuwamba. Haka dai aka rika kai da komo akan wannan shari’ar har ya zuwa halin da muke ciki yanzu. Duk wanda ya bi diddigin lamarin zai yi zaton cewar yana shaidar da wani wasa ne na kwaikwayo, in ba don ta’asar dake tattare da lamarin ba. Bayan zaman farko an sace daya daga cikin lauyoyin Saddam Hussein aka kashe shi. Kuma ba’ada bayan haka an kashe akalla mutane shida wadanda ke da dangantaka da shari’ar. Su kansu lauyoyin na Saddam hussein sun sha gabatar da kara a game da rashin samun wata cikakkiyar kariya dangane da makomar lafiyarsu. Ana sa ran cewar hukuncin da ake hasashen fitowarsa a farkon watan nuwamba zai kasance na kisa ne. Amma kuma hakan zai kara haddasa cece kucen da aka sha famar yi a game da halascin ita kanta shari’ar akan tsofon shugaban na kasar Iraki. Ba shakka lauyoyin Saddam Hussein zasu gabatar da kara akan hukuncin. A baya ga haka akwai daya shari’ar da aka fara akansa dangane da kisan kiyashin da aka yi wa Kurdawa, kuma wannan ba ita ce ta karshe ba akwai kararraki masu tarin yawa da za a gabatar da shari’a kansu, inda a takaice zamu iya cewa shari’ar ta Saddam Hussein zata ci gaba da tafiya ne har sai illa-masha’Allahu.