1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda bayan bude dandalin tunawa da yahudawan da aka kashe.

Hauwa Abubakar AjejeMay 10, 2006

Dandalin tunawa da yahudawa da aka kashe ya zamo daya daga cikin wuraren da masuz yawon bude idanu suke kai ziyara a birnin Berlin.

https://p.dw.com/p/Bu0D
dandalin holocaust
dandalin holocaustHoto: AP

Domin kuwa jamian dandalin sunce mutane miliyan 3 da rabi ne suka ziyarci dandalin a shekarar farko da aka bude shi.

Dandalin wanda BaAmurke Peter Eiseman ya tsara shi,wanda kuma aka bude shekara guda daya gabata,bayan muhawara na shekaru 17,an gina da nufin ci gaba da tunatar da jamaa kisan gilla na yahudawa miliyan 6 da yan Nazi sukayi.

Jamaa da dama dai na cewa ba don Wolfgang Thierse tsohon shugaban majalisar dokokin jamus ba,wanda kuma shine shugaban asusun kafa wannan dandali,mai muarabbain mita 20,000 da baa samu kamala kafa shi ba.

An dai kafa duwatsu kusan 2,000 domin tunawa da wadanda suka mutu,kodayake ba kowane yake goyon bayan kafa wannan dandali ba.

shekara guda bayan bude shi wannan dandali Wolfgang ya ziyarci gurin tare da wasu tsoffin yahudawa da suka tsere a zamanin Nazi daga Jamus,inda yanzu haka suke zaune a ingila,da kuma jikoki da yan uwan wadanda aka kashe.

Mahaifiyar Susie Kaufman,asalinta yar Jamus ce,kuma tana maida hankali ne akan wata kungiya ta yan gudun hijira yahudawa wanda aka kafa a 1941 ta kuma yaba da kafa wannan dandali.

Tace tana ganin kasaitaccen dandali ne,don yadda aka tsara shi,kuma ya baiyana abubuwanda suka faru,kodayake kowa yana da yadda zai fahimci maanar yadda aka gina shi,amma ganinta dandalin ya baiyana abubuwa daban daban ,kamar yadda aka kwashe mutane da kuma kashe su,ana ganin abin yana matukar kada zuciya”

Ana dai ci gaba da muhawara game da wannan dandali,wanda jamian dake kula da shi suka ce ya zuwa yanzu mutum kusan miliyan 3.5 suka ziyarta cikin shekara guda,domin gani yadda aka tsara shi,sai dai Susie Kaufman tace bai kamata dandalin na Holocust ya zama abin kallo kadai ba ga jamaa,kamata yayi ya zama abin tunani da taraddadin abinda ya faru ga yahudawa.

koda shike an kafa dandalin ne a kasar da tayi laifin kisan kiyashin ga yahudawa,amma shi kansa dandalin ba abu ne daya shafi jamusawa kadai ba,a daura da haka yana da alaka da sauran wuraren tunawa da yahudawa a biranen Washington da birnin Kudus.

Dandalin wanda aka kafa tsakanin kofar Barndenburg da kuma maboyar Hitler na karkashin kasa a tsakiyar Berlin yana dauke da tarihin dukkan yahudawa da suka rasa rayukansu a lokacin yakin Nazi anan Jamus.