1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda bayan Tsunami

December 27, 2005
https://p.dw.com/p/BvEr

A jiya ne miliyoyin mutane a kasashe daban daban na duniya suka gudanar da bukukuwan nuna alhini, na tunawa da mutanen da bala´in igiyar ruwa ta tsunami tayi wa lahani a matsayin shekara guda cif.

An dai gudanar da addu´oi da kuma shiru na dan mintuna a lokacin bukukuwan nuna alhinin don tunawa da wadanda suka rasa rayukan nasu.

Da yawa dai daga cikin mutanen da suka fi fuskantar lahani a lokacin wannan bala´i, sun fito ne daga wasu kasashe na Asia da kuma gabashin nahiyar Afrika.

An dai kiyasta cewa mutane sama da dubu dari biyu ne suka halaka wasu kuma ninkin haka suka jikkata kana, a daya hannun wasu miliyoyi suka rasa matsugunan kwanan su.