1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara tara bayan haren-haren 11 ga satumba

September 11, 2010

Ana ci gaba da fiskantar saɓani a Amirka dangane da shirin musulmi na gina ƙasaitaccen masallaci a birnin New-york.

https://p.dw.com/p/P9qH
Hoto: picture-alliance/dpa

A ƙasar Amirka, a daidai lokacin da ake juyayin cika shekara tara da haren-haren nan na 11 ga watan satumba da ya kashe mutane dubu uku, mahawara na ci gaba da zafafa dangane da gina masallaci a kusa da inda aka kai harin. Gangamin nuna goyon baya da kuma na nuna adawa sun fara gudana a kusan da tagwayen gine-ginen na birnin New-York da haren-haren suka ritsa da su.

Wannan dai shi ne karon farko da aka samu ruɗani irin daban daban tun bayan ƙaddamar da jerin hare-haren da ƙungiyar Al-qa'ida ta yi a wasu mahimman gine-gine na ƙasar Amirka. Barazanar ƙona alƙur'ani mai tsarki da pastor Terry Jones ya yi na daga al'amura da ke haifar da saɓani.

Shugaba Barack Obama na shirin isa ma'aikatar tsaron Amirka wato Pentagon domin halartan bikin nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren na sahekaru taran da suka gabata. An gudanar da addu'o'i a kusa da inda hare-haren suka wakana a birnin New-York.

Mawallafi:Mouhamadou Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala