1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekarar 2016 mafi tsananin zafi a tarihi

Gazali Abdou Tasawa
August 10, 2017

Sakamakon wani rahoton bincike kan dumamar yanayi a duniya ya nunar da cewa shekara ta 2016 ta kasance mafi tsananin zafi a duniya tun bayan soma aikin kididdigar yanayin zafi a shekara ta 1880.

https://p.dw.com/p/2i2Mr
Hitzewelle Italien
Hoto: Reuters/M. Rossi

Sakamakon wani rahoton bincike kan dumamar yanayi a duniya da wasu cibiyoyin nazarin sauyin yanayi suka wallafa a wannan Alhamis ya bayyana a shekara ta 2016 a matsayin mafi tsananain zafi da boren tekuna da yaduwar gurbattacciyar iskar gaz. Rahoton yace zafin ya kai kololuwar tsananin da duniya ba ta taba fuskanta ba tun daga lokacin da aka fara aikin tattara bayanan yanayin zafi a duniya a shekara ta 1880. 

Rahoton ya bayyana cewa ba a taba samun narkewar kankarar da ke a bagon Arewacin duniya ba dama ambaliyar ruwa da kuma fari da tsananin zafi kamar a shekaru biyu da suka gabata wato 2015 da kuma 2016. Rahoton ya kuma danganta wannan matsala da karuwar dumamar yanayi da kuma sauyin yanayin zafi na El Nino da aka fuskanta a farkon wadannan shekaru biyu. 

Wannan rahoto na zuwa ne mako daya bayan da kasar Amirka wacce ke a sahun gaba wajen fitar da hayaki mai gurbata muhalli a duniya ta tabbatar wa Majalisar Dinkin Duniya a hakumance  da matakinta na ficewa daga yarjejeniyar yaki da dumamar yanayi da kasashen duniya 195 suka sanya wa hannu a birnin Paris na kasar Farsansa.