1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

251108 10 Jahre Amadeu Antonio

Mohammad AwalDecember 3, 2008

Amadeu Antonio daga ƙasar Angola shi ne baƙo na farko da aka yiwa kisan gilla a nan Jamus bayan sake haɗewar gabashi da yammacin Jamus.

https://p.dw.com/p/G8Fp
Amadeu Antonio, wanda ´yan Nazi suka yiwa kisan gilla a Eberswalde a 1990.Hoto: Amadeu Antonio Stiftung

Yau dai shekara 10 ke nan da kafa gidauniyar Amadeu-Antonio don yaƙi da masu ƙyamar baƙi a Jamus. Amadeu Antonio daga ƙasar Angola shi ne baƙo na farko da aka yiwa kisan gilla a nan Jamus bayan sake haɗewar gabashi da yammacin Jamus. To sirin na yau zai duba ayyukan wannan gidauniya ne da nasarori ko akasin haka da ta samu shekaru 10 bayan kafuwarta.

Nasarorin da jam´iyar NPD mai matsanancin ra´ayin ƙyamar baƙi a nan Jamus take samu da zanen alamar ´yan Nazi a maƙabartun Yahudawa da fatattakar baƙi akan tituna da sauran nau´o´in ƙyamar baƙi da kai musu hare hare, munanan abubuwa dake ɓata sunan ƙasa. Alhaki ne ya rataya a wuyan ƙungiyoyin jama´a da su fito ƙarara su yaƙi waɗannan abubuwa. Tun shekaru 10 da suka wuce wata gidauniya mai suna Amadeu-Antonio mai mazauni a birnin Berlin ta ke yaƙi da masu ƙyamar baƙi. Wannan gidauniyar ta samu sunanta ne daga wani ɗan ƙasar Angola wanda ke zaman mutumin farko da ire-ire ta´asar da ake kaima baƙi bayan sake haɗewar Jamus ya rutsa da shi.

A cikin watan Nuwamban shekarar 1990 wani gungun matasa masu matsanancin ra´ayin ƙyamar baƙi suka yi masa kisan gilla a garin Erberswalde. Wannan gidauniyar da aka sa mata sunansa tana taimakawa a ayyuka daban daban musamman a ɓangarorin da suka shafi matasa da makarantu tare da ba da kariya da taimako ga waɗanda ta´asar masu ƙyamar baƙi ke rutsawa da su. Muhimmai daga cikin ayyukan wannan gidauniya sun haɗa da wayar da matasa kai da ƙarfafa musu guiwa wajen ƙirƙiro da nasu ƙungiyoyin a yankunan da suke.

Waƙoƙi don yaƙi da tsattsauran ra´ayin ƙyamar baƙi. Wannan dai wata dama ce ta samun ƙarin goyon baya don ƙarfafa yaƙi da wariyar launin fata da ƙyamar baƙi da masu ƙyamar Yahudawa. Ta wannan hanya ƙungiyar mawaƙa ta Brothers Keepers ke shiga cikin wannan fafatukar tare da ɗaukar makomarta a hannu kamar yadda ta nunar a shafinta na Intanet. Yanzu haka dai mawaƙa da masu fasahohi dake da dangataka da Afirka da kuma furodusoshi kimanin 90 sun shiga cikin wannan aikin wanda aka ƙirƙiro bayan kisan da ´yan ra´ayin Nazi suka yiwa Alberto Adriano ɗan ƙasar Mozambik a Dessau a lokacin bazarar shekara ta 2000.

Tun daga wannan lokaci ƙungiyar mawaƙa ta Brothers Keepers take waƙoƙin nuna adawa da wariyar jinsi da ƙyamar baƙi a cikin rayuwa ta yau da kullum. Tare da haɗin guiwar gidauniyar Amadeu-Antonio wannan ƙungiyar mawaƙa tana shirya bukukuwan kiɗe-kiɗe a makarantu dake gabashin Jamus. Daga shekarar 1998 zuwa yanzu sun gabatar da aikace-aikace kimanin 340 ƙarƙashin jagorancin tsohon kakakin majalisar dokokin Jamus Wolfgang Thierse. A matsayinsa na ɗan gabashin Jamus ya ce bai ga dalilin da zai sa a yi sake har masu gaba da demoƙuraɗiyya su samu gindin zama ba. Ya ce dole ne a yaƙe su ta kowace fuska.

“Shin ya kamata kuwa a ce ƙaruwar tashe tashen hankula da ƙyamar baƙi da yawaitar masu matsanancin ra´ayin ƙyamar baƙi dake ƙara zama ruwan dare, ya zama ladan da za mu same kenan bayan sake haɗewar Jamus da dukkanmu muka yi maraba da shi? Ai ko kaɗan haka bai dace ba.”

A matsayinta na wakiliyar gwamnati akan batutuwan da suka shafi baƙi, Anetta Kahane wanda ta girma a Berlin kuma take shugabantar gidauniyar Amadeu-Antonio tun da farko ta yi kashedi game da barazanar matsananci ra´ayin ƙyamar baƙi, kuma yanzu da kanta ta shaida yadda ake ƙara gane wannan batu yayin da a lokaci ɗaya matsala take ƙara yin tsanani. Ta ba da misali da bukukuwa tunawa da hare-haren bama-bamai da aka kan birnin Dresden, wanda yanzu ya zama wani dandalin masu son raya aƙidar Nazi na ƙasa da ƙasa.

“A cikin shekarun baya bayan nan an samu ƙaruwar yawan masu son raya manufofin ´yan Nazi a Turai baki ɗaya. Kimanin mutane dubu takwas suka halarci wannan gangami na masu wannan ra´ayi da ya gudana a birnin Dresden. Me yasa aka shirya wannan taro a Dresden? Bana adawa da gagarumin bikin da aka yi a wannan birnin na tunawa da waɗanda hare haren bama-bamai na sojojin ƙawance suka rutsa da su. Amma abin da ban ji daɗinsa ba shi ne rashin yin bayani game da abubuwan da suka janyo kai waɗannan hare-haren da kuma dangantakarsa ta tarihi. Hakazalika ba a kuma fito fili aka yi tir da abin da ´yan Nazi suka yi ba.”

Tun a wasu shekaru da suka gabata jam´iyar masu tsattsauran ra´ayin ƙyamar baƙi ta NPD wadda kotun kare kundin tsarin mulkin Jamus ke sa ido kan harkokinta, take da wakilci a majalisar dokokin jihar Saxony dake birnin Dresden. To sai dai Friedemann Bringt masani kan tsarin zamantakewa ya ce bai kamata majalisar ta zama tamkar wani dandanlin yaɗa ra´ayin ƙyamar baƙi ba. Friedemann na jagorantar wata ƙungiya dake bi ƙauye ƙauye tana wayar da kan jama´a game da haɗarin matsanancin ra´ayin nuna wariya.

“Irin wannan aiki na ƙungiyoyin jama´a kyakkyawan misali ne cewa za a cimma burin da aka sa a gaba. Amma hakan ba ya nufin kenan za a samu wani canji nan-take a harkokin zaɓe. Ganin yadda ake fitowa fili ana tattaunawa kan wannan batu wannan ci-gaba ne kan turbar da ta dace kuma za a samu nasara. Wani abin da ya burgemu shi ne yadda zaɓaɓɓen magajin garin ya fito fili ya yi magana kan wannan batu.”

Wani kyakkyawan misali shi ne a birnin Hamburg inda ake amfani da hanyoyi iri daban daban ciki har da waƙoƙi da wasan ƙwallon ƙafa don yaƙi da ´yan Nazi. Fitattun mutane daga dukkan fannoni na rayuwa suna tallafawa wannan aiki da kuma gidauniyar Amadeu-Antonio. To sai dai shugaban wannan yekuwa Jörn Menge ya ce bai gamsuwa ƙarancin goyon bayan da suke samu daga kamfanoni ba. Yace daga cikin kamfanonin 200 da suka nemi taimako daga garesu kashi 10 cikin 100 ne kawai suka ba su amsa.

“Da farko dai fargabar mu ita ce ka da mu rasa abokan hulɗar ciniki. Bai kamata ka bi hanyoyin da za su janyo koma-baya ga harkokinka na kasuwanci ba. Duk da haka ina mai ra´ayin cewa fitowa fili a yaƙi ´yan Nazi tamkar nuna adawa da masu keta haƙin bil Adama ne amma ba adawa da demoƙuraɗiyya ba.”

Masu wannan fafatukar sun ce ba za su yi ƙasa a guiwa ba musamman game da ´yan Nazi. Suka ce zasu ci-gaba da fafatawa har sai sun ga abin da ya turewa buzu naɗi.