1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

090710 Srebrenica UN

July 10, 2010

A wannan lahadin aka cika shekaru 15 da kewayowar ranar da aka yi wa dubun dubatan matasan musulmin Srebrenica na Bosniya Herzegovina kisan ƙare dangi.

https://p.dw.com/p/OG2j
Maƙabartar gama-gari a SrebrenicaHoto: DW

Gawawwakin mutane 6557 aka yi nasarar tantancewa daga cikin dubun dubatan gawawwakin matasan musulmin da aka tono daga kaburburan bai ɗaya a kan iyakar Sabiya da kuma Bosniya. Amma kuma adadin matasan musulmin da aka yiwa kisan gillar a Srebrenica ya ninka haka a wannan birnin da a wancan lokaci ke ƙarƙashin sa idon dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya. Daidai da ƙasashen Turai da suka shiga tsakanin Yugoslaviya da kuma Bosniya lokacin da suka gwabza ƙazamin yaƙin, sun kasa tantance yadda aka kai ga aiwatar ka kisan ƙare dangin na musulmi. Manjo janar Manfred Eisele, hafsan sojan Jamus da ya shugabanci sashen tsara dabarun wanzar da zaman lafiya a yankin na Balkans, danganta kisar kiyashin yayi da wani abu da ya samo tushe daga tarihi.

Gedenkfeier in Srebrenica Bosnien und Herzegowina Flash-Galerie
Zaman alhinin 'yan SrebrenicaHoto: AP

"Faɗace-faɗace da yankin Balkans ya fiskanta a farkon ƙarni na 20 ya taka mahimmiyar rawa wajen rura wutar rikicin. Ƙasashen Turai a wancan lokaci wato a 1995, sun yi ta takatsantsan bisa la'akari da mummunar ta'asar da ta auku a shekarar 1914."

A lokacin da aka tambayi shi janar Eisele na Jamus, ko MƊD na da ƙarfin hana aukuwar kisan kiyashin na musulmin Srebrenica, nuna shakku yayi. Dama wani bincike da wani ɗan jarida na ƙasar Holland ya gudanar, wato Huub Jaspers ya nunar da cewa MƊD ta ƙi amfani da angizon da ta ke da shi wajen hana kare rayukan musulmin na Srebreniva guda dubu 40.

"Kwamitin Sulhu na MƊD ne ke da alhakin abin da ya faru a Srebrenica. Membobin kwamitin sun sami bayanai daga ƙungiyoyin leƙen asiri da ke nuna cewa ana shirin farwa matasan musulmin. Amma kuma ba su ɗauki wani mataki domin hana aukuwar wannan kisan ƙare dangi ba. Babbar ayar tambaya a nan ita ce, mene ne dalili?"

Srebrenica 13 Jahre nach dem Massaker
Tunawa da bayaHoto: AP

A taƙaicen taƙaicewa, ƙasar Netherland aka fi aza ma laifin kisan kiyashin na musulmin Srebrenica, tun da a wancan lokaci ita ce ke shugabancin Kwamitin Sulhun MƊD. Ita ce kuma ta yi amfani da ƙarfin ikonta wajen hana tura sojojin samanta guda 450 zuwa filin daga domin guje ma jefa rayukansu cikin haɗari. Rashin bayar da izinin da ba ta yin ba ne ma, ya hana dakarun wanzar da zaman lafiya da ke Srebenica shiga tsakani. Sai dai lauyan wasu musulmin Srebrenica da suka tsira da rayukansu, da kuma suka shigar da ƙara gaban kotun duniya da ke birnin The Hague, ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya ma ba a baya take ba wajen rura wutar rikicin.

"MƊD na da nata laifin domin tana da hurumin ƙalubalantar matakin da Holland ta ɗauka. Amma ba ta yi ba. A saboda haka ya kamata MƊD ma a gurfanar da ita gaban kotun, domin ita da Holland ne suka gaza. Wannan larurar za ta ci gaba da damun 'yan asalin Srebrenica, matiƙar MƊD da Holland ba su roƙi gafara ba. Abin takaicin ma, shi ne rashin fara neman sasantawa da ba su yi ba."

Da yawa daga cikin dakarun na Netherland da suka kasance a Srebrenica a wancan lokaci sun haukace. Wasunsu kuma sun kashe kansu sakamakon gaza cetan rayukan bayin Allah da ba a ba su damar yi ba a Srebrenica.

Mawallafa: Selma Filipovic / Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Mohammad Nasiru Awal