1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 20 bayan faɗuwar katangar Berlin

Zainab MohammedNovember 4, 2009

Shin ko abubuwa sun daidaita tsakanin yankunan gabashi da yammacin Jamus shekaru 20 bayan sake haɗewa?

https://p.dw.com/p/KOHr
Ɗaukin murnar sake haɗewaHoto: picture alliance / dpa

Bayan wata ɗaya kacal da kammala bikin samun shekaru 40 da kafa ƙasar Jamus ta Gabas katangar da ta raba birnin Berlin gida biyu ta rushe a ranar bakwai ga watan oktoban shekara ta 1989. Kuma kusan shekara ɗaya bayan haka a daidai ranar uku ga watan oktoba sabbin jihohi biyar da aka sake kafawa a yankin Jamus ta Gabas suka shigga tutar tarayyar Jamus ta yamma. To ko shin yaya al'amura suka kasance a tsakanin waɗannan shekaru 20 bayan sake haɗewar ƙasar ta Jamus ƙarkashin tuta guda. Ahmad Tijani Lawal yayi nazari akan haka a cikin wannan rahoto...

Ko da yake a bisa taswira Jamus ta sake haɗewa ƙarkashin tuta ɗaya, amma fa har yau akwai banbance-banbance tsakanin gabaci da yammacin ƙasar in ji Friedrich Schrlemmer, malamin addinin kirista, wanda yayi shekara da shekaru a matsayin ɗan-Adawa a Jamus ta Gabas:

"Har yau sassan biyu sun yi hannu riga da juna, ko da yake sannu a hankali ana samun kusanta tsakaninsu. Na sikankance cewar nan da wasu shekaru ashirin masu zuwa kome zai daidaita."

Wannan maganar ta banbanta da kalaman da aka ji daga tsofon shugaban gwamnatin Jamus kuma madugun jam'iyyar Social Democrats(SPD) Willy Brandt a shekara ta 1989, wanda ya ce Jamus ƙasa ɗaya ce al'uma ɗaya kuma a saboda haka zasu bunƙasa tare da juna. Amma fa tuni murna ta koma ciki dangane da ɗaki da murnar da aka riƙa yi da farko in ji Friedrich Schorlemmer:

"Bayan ɗoki da taya juna murnar da aka riƙa yi shekaru ashirin da suka wuce, a yanzu an shiga wani hali ne inda al'amura suka kai wa mutane iya wuya inda ake fama da tafiyar hawainiya wajen kusantar juna."

Shi ma dai tsofon shugaban gwamnatin Jamus a wancan lokaci Helmut Kohl bai yi zaton za a sha fama da tafiyar hawainiya ba, lokacin da a shekara ta 1990 yayi wa 'yan gabacin Jamus alkawarin cewa:

"A haɗin kai zamu samar da wata ƙasa mai bunƙasa da yalwa."

Ita kuwa Angela Merkel a bikin zagayowar ranar sake haɗewar a ranar uku ga watan oktoban da ya wuce nuni tayi da cewar:

"Abubuwan da suka faru a wancan lokaci ba abubuwa ne da suka shuɗe suka zama tarihi ba. Ba wani babi ne na tarihi da aka rufe shi ba. Abu ne da ya shafi ainihin wani sabon babi na 'yanci da walwala wanda muke ciki a halin yanzu haka."

A shekara ta 1990 dai mutane kimanin miliyan 14 da dubu 500 ke zaune a gabacin Jamus, banda ma Berlin ta Gabas. Amma fa a yanzu yawan mazauna yankin bai zarce mutane miliyan 13 ba. Kuma ko da yake akwai dubban 'yan yammaci da kan koma gabacin Jamus da zama, amma an fi samun yawan masu ƙaura daga gabaci zuwa yammaci, inda a shekarar da ta gabata mutane kimanin dubu 50, musamman matasa da ƙwararrun ma'aikata suka tattara nasu ya nasu suka juya wa yankin baya. Waɗanda suka yi shaura su ne tsofaffi da marasa galihu. Babban dalilin jaka kuwa shi ne tafiyar hawainiyar da tattalin arziƙin yankin ke fuskanta. Bisa ga ra'ayin shugabar gwamnati Angela Merkel, muhimmin abu a yanzu shi ne shawo kan matsalar tattalin arziƙin duniya, mai yiwuwa ba'ada bayan haka a cimma nasara magance giɓin dake akwai tsakanin gabaci da yammacin Jamus.