1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 20 bayan kawar da mulkin Mobutu

Gazali Abdou Tasawa
May 16, 2017

An cika shekaru 20 bayan faduwar gwamnatin Shugaba Mobutu Sese Seko. Kawar da gwamnatin Mobutu dai ta biyo bayan tsawon shekaru 32 da ya shafe ya na mulkin kama karya a kasar.

https://p.dw.com/p/2d4K3
Rebellen eroberen Kinshasa - Mobutu auf der Flucht
Hoto: picture-alliance/dpa/Feferberg

A ranar 14 ga watan Oktoban shekara ta 1930 ne aka haifi Mobutu Sese Seko a garin Lisala na kasar Kwango da ke a karkashin mulkin mallakar Turawan kasar Belgiyam. Tun da kurciyarsa ne ya dukufa wajen yi wa kasa aiki inda tun a watan Yulin shekara ta 1960 ya zamo sakataren kasa a gwamnatin Patrice Lumumba a lokacin ya na dan shekara 30 da haihuwa.

Shekaru biyar bayan haka ne Mobutu ya kifar da gwamnatin shugaban kasar na farko Joseph Kasa-Vubu a ranar 24 ga watan Nowambar shekara ta 1965. Hawan sa mulki ke da wuya ya bayyana bukatar raba gari da duk wasu al'adu da 'yan kasar suka gado daga Turawan mulkin mallaka inda alal misali ya umurci 'yan kasar da saka wa 'ya'yansu sunaye na asali na kasar.

Mobutu Sese Seko
Mobutu Ya shafe shekaru 32 ya na mulki Jamhuriyar Dimrokradiyyar Kwango wadda a baya ake kira da suna Zaire.Hoto: AP

Baya ga wannan, shugaban ya kuma sake rada wa kansa suna inda ya kira kansa Mobutu Sese Seko Kuku Ngbendu wa za Banga, wanda ke nufin Mobutu jarimin yaki da ke samun nasara bisa nasara ba tare da wani ya iya taka masa birki ba. Daga nan kuma ya rikide zuwa mulkin kama karya inda ya yi fice wajen kame-kamen masu adawa da mulkinsa da gana masu azaba kafin hallaka su daga karshe.

Sai dai duk da irin yadda ake kallonsa a matsayin dan kama karya, Mobutu ya kasance mai alfahari da kasarsa, lamarin da shi ne ma ya haifar da zaman doya da man ja na tsawon shekaru da shugabannin da suka mulki Faransa. Kazalika ya yi kokarin kare martabar kasarsa a gaban kusan dukkanin kasashen Turai.