Shekaru 20 bayan rushewar katangar Berlin
Taya juna murna
A cikin ɗauki da mrna mutane suka shiga rungumar juna a bakin iyakar (a hoto: wasu ma'aurata ne daga gabashin Jamus).
Wajibi ne a kawar ga wannan katanga
Dubban masu zanga-zanga gabanin rushewar katangar a gabashin Berlin sun shiga ihu da cewar:"Wajibi ne a kawar da wannan katangar. Mutane da dama a Berlin suka ƙuduri niyyar ba da tasu gudummuwar kuma nan take suka kama aiki.
Rushe katangar
Da wasu 'yan ƙananan kayan aiki mutane suka shiga ƙoƙarin rushe katangar suna masu watsi da kiran da 'yan sanda ke yi musu da su "daina buge-bugen bangon nan take. An dai laƙaba musu sunan "Masu Rushe Bango".
Kama hanya zuwa yammaci
Tare da tafi da guɗa aka shiga marhabin lale da 'yan gabashin Jamus dake kutsawa ta mararabar iyaka ta Checkpoint Charlie. Bayan buɗe iyakokin 'yan gabashin Jamus sun samu wata dama ta farko ta shigowa Jamus ta Yamma ba tare da nuna wani dalili ba.
Tuntuɓa ta farko
A ranar 10 ga nuwamban 1989: Wani ɗan Berlin na musafaha da jami'an tsaron iyakar gabashin Jamus su biyu a kusa da mararabar "Checkpoint Charlie".
Leƙe ta katanga
Jami'an tsaron iyakar gabashin Jamus na leƙen masu zanga-zanga ta wani ramin da aka huda a katangar.
Cunkoso akan katanga
Dubban mazauna Berlin, a yammacin 9 ga watan nuwamban 1989 suka runtuma zuwa Brandenburger Tor suka taru a gefe da kuma a kan katangar.
Biki kai tsaye
A kan iyaka tsakanin gabashi da yammaci mutane sun shiga shagulgula game da buɗe iyakokin da aka yi.
Ganima
Wasu matasa su biyu na alfahari da guturen katangar ta Berlin tamkar ganima.
Ɗauki da murna
Nasara: Jamusawa daga gabashi da yammaci na biki akan katangar da ta raba su tsawon shekaru 28. A maraicen 9 ga nuwamba aka buɗe katangar Berlin. Hakan ya zama matakin farko game da rushewar Jamus ta Gabas.
Ɗarewa kan katanga
'Yan gabashin Berlin sun riƙa haua kan katangar mai tsawon mita 3.6 a jajibirin 10 ga nuwamba.
Jama'a na shagulgula
A yammaci: A ranar 10 ga nuwamban 1989 mutane sun yi cincirindo kan katangar a gaban majalisar Reichstag, inda a yau majalisar dokoki ta Bundestag ke da mazauninta. An dai shirya shagulgula iri daban-daban a faɗin Berlin domin tunawa da abubuwa na tarihin da suka wakana shekaru 20 da suka wuce.