1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 40 da boren dalibai a Soweto a Afirka ta Kudu

Thuso Kumalo/ LMJJune 16, 2016

Jami'an tsaro sun bude wuta tare da kashe daruruwan 'yan makaranta masu zanga-zangar nuna adawa da sanya harshen Afrikaans a matsayin harshen koyarwa a makarantun kasar.

https://p.dw.com/p/1J8Eo
Südafrika 40 Jahre nach dem Schüleraufstand von Soweto
Bikin addu'o'in tuna wa da wadanda aka kashe a boren na SowetoHoto: picture-alliance/AP Photo/T. Hadebe

A wannan Alhamis din aka cika shekaru 40 da yin zanga-zangar Soweto na kasar Afirka ta Kudu, wanda aka yi a ranar 16 ga watan Yuni na 1976. Jami'an tsaro na gwamnatin wariyar launin fata sun bude wuta a kan daliban inda suka hallaka akalla yara 'yan makaranta sama da 600 da suka yi zanga-zangar nuna kin amincewarsu da sanya harshen Afrikaans, a matsayin wanda za a rinka koyarwa da shi a makarantun kasar. A cewar wadanda suka tsira yayin wannan arangamar dai, sadaukarwar da daliban suka yi a shekarar 1976 ce sanadiyyar bunkasar Soweto da kuma 'yantacciyar Afirka ta Kudu.

A sanyin safiyar ranar 16 ga watan na Yuni na 1976 ne dai daruruwan yara a Soweto suka yi bankwana da iyayensu tare da tafiya makaranta, ba tare da sanin cewa wasu daga cikinsu sun yi bankwanan karshe da iyayen nasu ba. Daliban da ke manyan ajujuwa sun fara karfafa wa sauran na kasa da su gwiwa kan su fito su shiga tattaki domin nuna adawarsu da tilasta koyarwa a makarantu da harshen Afrikaans.

Südafrika 40 Jahre nach dem Schüleraufstand von Soweto
Sam Nzima rike da hoton yaron nan dan shekaru 13 Hector Pieterson lokacin da aka harbe shiHoto: picture-alliance/AP Photo/D. Farrell

Murphy Morobe na daya daga cikin shugabannin daliban da suka shiga wannan zanga-zanga ta lumana ya kuma bayyana dalilinsu yana mai cewa:

"Muzguna wa tsiraru shi ne masu cin zali su tilasta wa wadanda suka gallazawa yin amfani da harshensu. Mun yi tunanin abu ne da ya kamata mu nuna tirjiya a kai."

'Yan sanda sun bi umurnin yin kisa

Sai dai yayin da suka isa kan hanyar Vilakazi da ke Orlando ta Yamma, 'yan sandan gwamnatin wariyar launin fata sun bude musu wuta. Sam Nzima, shi ne ya dauki hoton dan shekaru 13 a duniya Hector Pieterson, ya ce har yanzu yana tuna yadda 'yan sandan suka rinka yin kisa, inda ya ce umurni kawai aka basu su bude wuta kan mai uwa da wabi, ya kuma tuna sanda dan karamin yaro ya fadi kasa a mace. Kisan dai ya yi tabo a zuciyar 'yan uwa da abokan arziki na wadanda suka rasa rayukansu.

Antoinette Sithole 'yar uwa ce ga Pieterson, da aka kashe yana da shekaru 13 a duniya ta kuma bayyana yadda ta ji tana mai cewa:

"Lokacin da na kalli kanina jini na fita daga bakinsa na shiga firgici. Lokacin da wani ke sa shi cikin mota sai na ji ya ce: Oh ya rasu. Ina jin haka sai na fashe da kuka cikin dimuwa."

Südafrika Hector-Pieterson-Mahnmal in Johannesburg, Soweto
Dandalin mutum mutumin Hector Pieterson a birnin JohannesburgHoto: Imago/imagebroker

Seth Mazibuko, na da shekaru 16 a yayin da ya shiga cikin wannan tattaki a shekarar ta 1976, ya ce sun shiga firgici ganin yadda 'yan sanda ke musu harbin kan mai uwa da wabi.

Ya ce: "Ba mu taba tunanin za su yi kisa ba balle ma har su yi ta kisan yara kanana haka."

Boren Soweto ya taka rawar kawo sauyi

Bayan wannan kisan kiyashin da aka yi musu dai, dalibai da dama sun tsere daga kasar tare da daukar makamai kana suka dawo domin kwatar 'yanci a shekara ta 1994. Sai dai har yanzu akwai wadanda ba su kara jin duriyar yaransu ba. Shekaru 40 da afkuwar kisan, amma har yanzu suna cikin damuwa kuma ba su fitar da ran sake ganinsu ba.

Ga da dama daga mazauna Soweto dai na jinjina wa daliban kan sadaukarwar ta shekarar 1976. Oupa Moloto na daya daga cikin daliban da suka shirya zanga-zangar, kana shugaban gidanuniyar 16 ga watan Yuni na shekarar 1976 a Soweto, ya kuma ce Soweto da Afirka ta Kudu sun samu ci gaba ne sakamakon sadaukarwar da suka yi.

Sai dai wasu na ganin cewa duk da sadaukarwar da yaran suka yi ta taimaka wajen kawo 'yancin dimokaradiyya, amma har yanzu 'yan Afirka ta Kudu na baya a fannin 'yanci na tattalin arziki.