1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 50 da tawayen Hungary

Hauwa Abubakar AjejeOctober 23, 2006

shugabannin manyan kasashen duniya da dama suka hallara yau a kasar Hungary,don taya su tunawa da zagayowar shekaru 50 da kisan gilla da tankunan tsohuwar taraiyar Soviet sukayi a kasar a 1956,yayinda a daya hannun kuma harkokin siyasar kasar suka shiga rudani.

https://p.dw.com/p/Btxd
Hoto: AP

Bikin na yau dai ya fara ne cikin tashe tashen hankula inda matasa suka kara da yan sanda,inda aka tsare wasu daga cikin masu zanga zangar,wasu kuma aka bar su jina jina.

An gudanar da bikin ne a bakin majalisar dokokin kasar inda manyan baki suka hallara domin tunawa da wannan rana da jamaar kasar sukayi wani bore,wanda sojojin tsohuwar taraiyar Soviet suka kwantar da shi da tankunan yaki.

Shugabannin da suka halarci bikin sun hada da shugaban kasar Hungary Laszlo Solyom da firaminista Ferenc Gyurcsny,tare da wasu shugabanin kasashen turai 18,da firaministoci 2,da sarkon Norway da kuma shugabannin hukumar turai dana kungiyar tsaro ta NATO.

Tawayen na Hungary ya barke ne a ranar 23 ga watan oktoba na 1956,sai a ranar 4 ga watan oktoba ne kuma tankunan Soviet suka kwantar dashi,inda daga nan kasar ta koma karkashin Soviet har zuwa rushewarta a 1989.

Tawayen ya fara ne da zanga zangar lumana na dalibai shekaru 50 da suka shige,wadda ya rikide ya hade kan kwarraru,dalibai maikata da manoma da suna masu neman yancin kansu daga shekaru na mulkin zalunci.

Daya daga cikin daliban da suka gudanar da zanga zangar Peter Pallay ya baiyana yadda sukayi.

“ mun kwarara kan tituna karo na farko a rayuwarmu ba tare da neman izni daga sama ba kuma mun baiwa dukkan jamaar Budapest mamaki.kasa cw wadad ta zamo daya,wato yanci ne dab a zaa iya misalta shi ba,bag a kowace kasa hakan yake faruwa ba”

yan kasar Hungary 2,800 suka rasa rayukansu a lokacin zanga zangar wasu da dama suka jikkata,yayinda dubbansu suka tsere zuwa yammacin nahiyar.

Yayinda shugabannin kasashen duniya suka hallara taya yar karamar kasar murnar samun yancin kanta,rudani cikin banbancin raayi na siyasar kasar na neman mamaye wannan biki.

Domin kuwa babbar jamiyar adawa ta janye daga halartar bikin domin firaministan Gyursany zaiyi jawabi wajen bikin.

Jamiyarasa ta socialist ce dai ta gaji jamiyar yan kominist bayan komawa kasar ta Hungary tafarkin demokradiya a 1989.

Jamiyar ta adawa ta jingina karya da firaminsitan yace yayi ne a lokacin yekuwar neman zabe kafina sake zabensa.

Wannan mataki da jamiyar adawa ta dauka ya mamaye bikin na tunawa da tawayen 1956,wanda ya fara da zanga zangar lumana ta dalibai,kafin ya rikide zuwa babban tawaye game da zalunci na zamanin Stalin,inda dalibai da manoma da kuma maaikata suka bukaci yancin kansu bayan shekaru na zalunci da ake masu.

Jamiyar ta Fidesz shekaru da dama bata gudanar da bikin tunawa da tawayen tare da jamiyar socialist saboda a cewarta,jamiyar ta gaji jamiyar yan kominist data hada kai da taraiyar Soviet a 1956.

A halin da ake ciki dai yanzu kafofin yada labaru na Hungary sun sanarda cewa masu zanga zangar a birnin Budapest sun kame wata mota tanka da aka ajiye a wani wuri na musamman don tunawa da wannan rana,inda suka tuka ta zuwa inda yan sanda suke.

Yan sandan sun haraba borkonon tsohuwa da harsashen roba da na ruwa kan masu zanga zangar inda da dama daga cikinsu suka samu rauni.