1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 60 bayan kafa Majalisar Dinkin Duniya, ina aka nufa ?

YAHAYA AHMEDOctober 24, 2005

A cikin wannan shekarar ne Majalisar Dinkin Duniya ta cika shekaru 60 da kafuwarta. Kuma, a ran 24 ga watan Oktoban shakarar 1945 ne kundin tsarin manufofinta ya fara aiki. Ko me aka cim ma a cikin wadannan shekaru 60 ?

https://p.dw.com/p/Bu4f
Hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da tutocin wasu daga cikin kasashe mambobinta a birnin New York.
Hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da tutocin wasu daga cikin kasashe mambobinta a birnin New York.Hoto: AP

Kundin tsarin ka’idojin gudanad da aikin Majalisar Dinkin Duniya ya fara ne da wannan baiti: „Mu, `yan Majalisar dinkin Duniya“. Amon baitin dai nja da dadin ji. Amma bisa dukkan alamu kwaskwarima ce kawai. Saboda, gwamnatocin da ke yanke shawara kan inda majalisar za ta mai da alkiblarta, duk sun kasa cim ma daidaito kan batutuwa da dama da suka shafi kafar. Bugu da kari kuma, ba duk gwamnatocin ne na dimukradiyya ba. Akwai gwamnatoci da yawa, masu tafiyad da mulkin kama karya, wadanda har ila yau ake damawa da su wajen tsai da muhimman shawarwari kan harkokin majalisar. Gwamnatocin da aka zaba bisa tafarkin dimukradiyya ma, ba lalle ba ne su bi ra’ayin jama’ar da suka zabe su wajen ka da kuri’a a kwamitin sulhu na Majalisar, a kan muhimman batutuwan da za a zartad da kuduri a kansu. A lal misali, Firamiyan Birtaniya Tony Blair da na kasar Spain a lokacin yakin Iraqi, José María Aznar, sun yi amanna da gudanad da yakin, duk da cewa mafi yawan `yan kasarsu na nuna matukar adawa ga shirin hambarad da Saddam Hussein.

A lokacin yakin cacar baka kuma, kwamitin sulhun bai iya ya aiwatad da manufofin da suka sa ma aka kirkiro shi ba, wato na tabbatad da ganin cewa, an samad da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Duk da kokarin da sojojin kare zaman lafiya da majalisar ke turawa a yankunan da rikici suka barke ke yi, ba za a iya cewa kwamitin sulhun ya cim ma burinsa ba. Saboda kawo yanzu, ba a girke su ma a yankunan sai bayan rikicin ya barke har al’amura kuma sun tabarbare. A galibi, majalisar ta gaza wajen hana barkewar yaki, kamar yadda misalan Korea da Vietnam ke nunawa. Kazalika kuma, a Ruwanda, an gudanad da mummunan kisan kiyashi ne, yayin da duniya ta sa ido tana kallo.

Tun da aka kawo karshen yakin cacar baka tsakanin rukunan Gabas da na Yamma a karshen shekarun 1980, an yi ta samun ragowar masu hawar kujerar na ki a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar. Amma misalin Iraqi na nuna cewa, wannan muhimmiyar kafar ta Majalisar, ba z ata iya hana aukuwar yaki ba, sai duk mambobinta masu kujerar dindindin sun yarje kan hakan.

Da dai an bi shawarwarin da babban sakkataren Majalisar Kofi Annan ya gabatar ne, da a lokacin bukukuwan cika shekaru 60 da kafuwarta, an yi wa tsarin Hukumar gaba daya kwaskwarima, don ta iya bunkasa ayyukanta da kuma magance kalubalen da take kara huskanta a cikin wannan karnin na 21. Amma me ya faru ? A taron kolin da aka gudanar a cikin watan Satumban da ya gabata, babu wani sahihin sakamakon da aka cim ma kan wannan batun. Duk shugabannin kasashen Majalisar sun bayyana shirinsu ne na amincewa da manufar nan ta cimm ma burin rage yawan talauci a duniya zuwa rabinsa na shekara ta 2000 kafin shekara ta 2015. Amma a zahiri, idan aka zo ga ba da kudade da gudummuwa don aiwatad da manurfofin, sai ka ga kasashen da suka yi alkawarin na dari-dari, ko kuma tafiyar hawainiya. A kan batun yi wa kwamitin sulhun kwaskwarima ma don fadada shi, babu abin da aka cim ma. Haka kuma, an kasa yarjewa kan yadda za a ba da ma’anar ta’addanci. A nan dai za a iya ganin yadda cim ma daidaito zai yi wuya, wajen tsara wa majalisar kyakyawar makoma.

A halin da ake ciki yanzu dai, ana nesa da burin samar wa duniya baki daya hukumar zartaswa, wadda za ta maye gurbin Majalisar.