1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 70 bayan harin nukiliyar Hiroshima

Usman Shehu Usman/ASAugust 6, 2015

A Wannan Alhamis din ce (06.08.2015) ake bikin tunawa da jefa makamin nukiliya a Japan shekaru kimanin saba'in da suka gabata. An dai kai wannan hari ne a birnin Hiroshima.

https://p.dw.com/p/1GBA4
Bildergalerie Hiroshima Nagasaki Atombombe 1945
Hoto: Courtesy of the National Archives/Newsmakers

Duk da cewar an shekara 70 da jefa makamin nukiliya a kasar Japan, har yanzu duk lokacin da aka ambaci garuruwan da makamin ya fada wato Hiroshima da Nagasaki, ana tuna irin illa da makamin ya yi. Mutane da damar gaske ne suka mutu sanadiyyar makamin nukilyar da Amirka ta jefawa Japan a biranen biyu.

Shugabannin kasar Amirka na wancan lokacin sun kera makamin karkashin wani shirin da aka yi wa suna "Shirin Manhathan" inda aka yi amfani da sinadarin uranium da dalma wajen kera makamin na kare dangi na farko da aka taba gwadawa kan bil Adama a duniya.

Bildergalerie Atomwaffen 66 Jahre Hiroshima Atombomben Sprengung in Nevada USA
Hoto: AP

Masana kimiyya da damar gaske ne suka yi aiki wajen kera makaman kare dangin da aka yi amfani da su a Japan din, inda aka rarrabasu a masana'antu daban-daban da ke fadin Amirka. Bugu da kari shirin ya dau ma'aikata sama da 125,000 wadanda ke gudanar da binciken kimiya daba-daban domin dai a tabbatar an samar da makamin.

An kebe makarantu na musamman inda aka killace masanan domin su bada himma kan aiki da kuma watakila gudun kada su yada sirri na yadda ake kera makamin, domin a lokacin manufar shirin shi ne a hanawa Rasha mamaye kasar Japan.

Bildergalerie Hiroshima Nagasaki Atombombe 1945
Hoto: Kazuhiro Nogi/AFP/Getty Images

Yayin bikin na bana wanda ya samu hallartar mutane da dama daga ciki da wajen Japan din, an gudanar da jawabai da addu'o'i iri-iri musamman ma dai a wajen da aka jefa makamin shekaru 70 da suka gabata lokacin da ake yin yakin duniya na biyu.