1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 8 na dimokradiyya a Nigeria

May 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuKY

Shirye shirye sun kammala a Nigeria, dangane da rantsar da Alh Umaru Musa Yar´adua a matsayin sabon shugaban kasar. Kasa da awowi 24 a fara bukukuwan rantsuwar, har yanzu da yawa daga cikin yan kasar na kallon nasarar ta Alh Yar´adua, a matsayin magudi ne kawai.Kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida dana waje na zargin Shugaba mai barin gado ne, Cif Obasanjo da shirya magudin daya bawa jam´iyyar su ta PDP nasara, a zaben na gama gari daya gabata.Wannan dai shine karo na farko da wata gwamnatin farar hula zata mika mulki´, hannun wata farar hulan a tsawon tarihin kasar ta Nigeria.