1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru biyar bayan mamayar Iraki

Shuaibu Othman SamboMarch 8, 2008

Rayuwar jama'ar Iraki shekaru biyar bayan mamayar kasar da Amurka ta jagoranta

https://p.dw.com/p/DL8c
Hare -hare da zubadda jini da ke faruwa a IrakiHoto: AP

A lokacin da ake ƙara kusantar cika shekaru biyar da sojojin taron dangi ƙarƙashin jagorancin ƙasar Amurka da suka mamaye Iraqi a ranar 19 ga watan Maris ɗaukacin mutanen Iraqi na bayyana cewa sun zama raɓa dani a ƙasarsu domin kuwa suna takure .

Bayan ɓacewar abin da aka fi sani da natsattsiyar rayuwa irin ta yau da kullum a ƙasar Iraqi,al'ummar garin Bakuba sun sami kansu a cikin halin ƙunci da taɓarɓarewar rayuwa.

A cewar wani ɗan ƙasar mai suna Bashar Ameen ya ce An wayi gari mutane sun manta da yadda ake jin daɗi saboda kulum wuya kawai ake sha

Hatta a ranakun shagulgulan sallah guda biyu na musulunci;wato sallah ƙarama da babba waɗanda a bisa al'ada lokatai ne da mutane kan ci kwalliya da sababbin kaya su gyara gidajensu a haɗu ana farin ciki da annashuwa da sada zumunci a tsakanin 'yan uwa da abokan arziƙi,yanzu waɗannan ranaku sun zama ranakun ƙunci ga jama'ar,ba domin komai ba sai saboda irin matsaloliln da jama'a ke fuskanta na fashewar bama-bamai ko dai hare hare na ba gaira babu dalili.

Aiman Nory wani ma'aikaci a Hukumar ilimi ta ƙasar Iraqi ya ce `Bukukuwan da aka yi na baya-bayan nan ma ba su shirya ko kuma tanadi komai ba domin ganin ba wani abin farin ciki da annashuwa kamar yadda aka saba a baya`


Ƙanan yara waɗanda da zarar lokacin wani shagali ya matso zaka ga suna ta ɗoki, suma duk sun manta da irin waɗannan abubuwa.A da kafin Amurka ta mamaye ƙasar Iraqi za ka ga kowane saƙo da kwararo cike da jama'a , yara na ta wasanni,iyalai na kaiwa da komowa to amma yanzu duk babu`


A bisa al'ada mutanen ƙasar Iraqi sukan baiwa shagulugula mahimmanci musamman ma dai ta ɓangaren da ya jibanci ciye-ciye da shaye-shaye a lokutan bukukuwa, hatta ma a tsakanin shekarun 1990 sa'adda aka sanyawa ƙasar takunkumin tattalin arziki,al'ummar Iraqi sun cigaba da irin waɗannan al'adu nasu musamman ma dai a ranakun juma'a.


To amma yau fa an wayi gari waɗannann abubuwa duk sun fara dushewa tamkar ba a yinsu ,sabo da halin rashin tsaro da tsadar rayuwa, da kuma matsanantan dokokin a harkokin yau da kullum.Wanda Mutanen ke jin cewa ya mayar da su tamkar wasu fursunoni a ƙasarsu a sakamakon rashin walwala.Kai bama Mutane ba kawai hatta layuka da gine-gine suma duk sun taɓarɓare banda kango,taɓo da datti a tituna da rusassun gidaje da karyayyun bishiyoyi ba ka ganin komai inji wani injiniya da ke garin Baquban '


A cikin watan Janairun wannan shekara ce dai shugaban hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijira Antonio Gutteries, ya bada sanarwar irin wahalhalun da yan ƙasar Iraqi da ke gudun hijira a ƙasar Siriya ke fuskanta. Wani nazari da hukumar ta gudanar ta hanyar ganawa da wasu 'yan gudu hijira 754, ya bayyana cewa kimani kashi 90 cikin ɗari na fama da damuwa,70 kuma na fama da firgicin abin da ya faru dasu har yanzu.


kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya sybella wilkes, ta ce ba su yi mamakin ganin wannan sakamako ba saboda halin da sansanin yan gudun hijiran da ke ƙasar siriya ya nuna.


Ana ganin haka zata iya faruwa ma ga mazauna cikin ƙasar Iraki a yanzu haka,domin kuwa sama da shekaru biyu kenan da Likitici a Iraqi ke gabatar da rahotonni game da irin Karuwar da ake samu na amfani da ƙwaya barkatai domin kwantar da hankali ko samin ƙarfi.