1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

280409 5. Jahrestag EU-Osterweiterung

May 1, 2009

Faɗaɗa ƙungiyar EU a ranar ɗaya ga watan Mayun 2004 shi ne mafi girma.

https://p.dw.com/p/HiIw
Shugabannin ƙasashe goma da EU ta ɗauke su a shekarar 2004Hoto: AP

Kawo yanzu matakin faɗaɗa ƙungiyar tarayyar Turai a shekara ta 2004 shi ne mafi girma, domin bayan da dukkan al´ummomin ƙasashen ƙungiyar suka yi na´am da wannan mataki a ƙuri´un raba gardama, a ranar ɗaya ga watan Mayun shekara ta 2004 an shigar da ƙasashen Estoniya, Latvia, Lituaniya, Malta, Poland, Slovakiya, Slovaniya, Czeck, Hungary da kuma Cyprus a cikin ƙungiyar. Hakan ya sa yawan membobin ƙungiyar ya ƙaru ya zuwa 25 kafin sake faɗaɗa ta a ranar ɗaya ga watan Janerun shekara ta 2007 inda aka shiga da ƙasashen Bulgariya da kuma Romaniya.

A daren ɗaya ga watan Mayun shekara ta 2004 an yi bukukuwa irin daban daban a dukkanin sabbin ƙasashen da aka shigar da su cikin ƙungiyar ta tarayyar Turai EU, kamar a yankin kan iyakar ƙasar Jamus da Poland.

Wannan rana dai ta kasance ta musamman ga tsohon ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer wanda yayi jawabi a yankin kan iyakar ta Jamus da Poland.

"A wannan yammacin na yau an samu sabuwar nahiyar Turai da kuma wani yanki na wanzuwar zaman lafiya. A wannan yammacin an samu wata nahiyar Turai wadda makomarta ke da muhimmanci a gare mu. Saboda haka dole mu yi shagalinmu."

To sai dai ba kowa ne ya yi maraba da haka ba. Alal misali Jamusawa da yawa sun nuna fargabar cewa za su fuskanci gogayya da ma´aikata daga gabashin Turai wanda haka zai jefa rayuwarsu cikin halin ƙaƙa-ni-kayi. Jim kaɗan gabanin ɗaukar ƙasashen tsohon shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya yi ƙoƙarin kwantarwa ´yan ƙasarsa da hankali.

"Matsalolin da ka iya kunno kai kamar a kasuwar ƙwadago ko a fannin yiwa jama´a hidima ko aikata manyan laifuka, tuni da ma muna fama da su gabanin faɗaɗa ƙungiyar EU kuma za mu wahala wajen magance su idan ba mu faɗaɗa ƙungiyar ba. A gare ni yana da muhimmanci idan aka fahimci wannan."

Jamus da sauran tsofaffin ƙasashen EU sun ɗauki matakai na dakatar da kwararowar ´yan ci-rani daga sabbin membobin ƙungiyar tsawon wasu shekaru. Ko da yake ba bu wata hujja game da fargabar da ake nunawa amma sannu a hankali an fara nuna gajiyawa dangane da faɗaɗa ƙungiyar. A shekarar 2006 an jiyo shugaban gwamnatin Austriya Wolfgang Schüssel yana mai kira da a yi la´akari da wannan batu. Inda ya ce shirin faɗaɗa EU yana da iyaka.

Duk da haka an ɗauki ƙasashen Romaniya da Bulgariya a shekarar 2007, to sai dai adawa da sabbin membobin ya ci-gaba da wanzuwa. A dangane da haka ya sa aka kasa warware batun yiwa EU kwaskwarima kamar yadda yarjejeniyar birnin Lisbon ta tanada. A lokacin da ya karɓi shugabancin EU a tsakiyar shekarar 2008, shugaban Faransa Nikolas Sarkozy cewa yayi.

"Ana buƙatar yarjejeniyar Lisbon domin a faɗaɗa Turai. Idan ba wannan yarjejeniya to sai a koma ga yarjejeniyar birnin Nice wadda ta ƙi faɗaɗa ƙungiyar EU fiye da ƙasashe 27 ba tare da yiwa hukumomin ƙungiyar canje canje ba."

Matsalar kuɗi da tattalin arziki da ake fama da su yanzu na ƙara dagulawa sabbin ƙasashen EU al´amura sannan suna ƙara zam wani nauyi ga tsofaffin membobin.

Ko da yake yanzu babu wata gwamnati ta EU dake saka ayar tambaya game da matakin na shekara ta 2004 to amma tuni ɗokin samun wata kyakkyawar nahiyar a ranar ɗaya ga watan Mayun 2004 ya dushe.

Mawallafa: Christoph Hasselbach/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala