1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru biyar na yakin basasa a Siriya

Anne Allmeling/AS/USUMarch 15, 2016

A watan Maris da muke ciki ne rikicin da ya fara da boren masu adawa da shugabancin Bashar al-Assad ya shiga shekara ta biyar

https://p.dw.com/p/1IDVG
Damaskus Baschar al-Assad AFP Interview
Hoto: Getty Images/AFP/J. Eid

Boren kin jinin gwamnatin Assad ya fara a tsakiyar watan Maris na shekarar 2011, inda masu zanga-zanga suka fara rajin ganin ya sauka daga gadon mulki don a samu sukunin yin gyare-gyare a tsarin tafiyar da kasar ta Siriya. Da dama dai ba su dauka za a kawo wannan loakci ba tare da samun sauyin shugabanci a kasar ba, kamar yadda aka gani a kasashen Tunisiya, Yamen, Masar da Libya, biyo bayan guguwar neman sauyi ta kada a kasashen Larabawa.

To sai dai sabanin sauran kasashen Larabawa da aka nemi samun sauyin shugabaci, a Siriya lamura sun dauki wata alkibla ta daban, inda kungiyoyin da ke dauke da makamai da ke goyon bayan gwamnati da sojoji da kuma 'yan adawa da nasu kungiyoyin, musamman ma Free Syrian Army a daya hannun, suka yi ta dauki ba dadi wanda haka ya rikide zuwa halin da ake ciki yanzu.

A cikin watan Yulin shekara ta 2013 ne dai kungiyoyi irinsu Hezbollah ta Lebanon, suka shiga yakin na Siriya har ma shugabanta Hassan Nasrallah ya ce za su yi bakin kokarinsu wajen dafawa Assad baya don ganin ya ci-gaba da kasancewa kan a mulki.

"Ya ce idan muna da mayaka 100 to za mu kara yawansu zuwa 200, in kuma 500 to za su zama 1000. Kai in ya kama ni da dukannin 'yan Hezbollah mu shiga Siriya, to za mu je don yin wannan yakin da nufin kare kasar daga tada kayar bayan tsageru.

To haka dai yakin ya cigaba da gudana, inda masu adawa da gwamnati suka fara kame wasu sassan kasar ciki kuwa har da birnin Aleppo da ke zama cibiya ta kasuwaci, kuma ya ke da muhimmanci gaske ga gwamnatin Assad. Daga bisani kasashen duniya ciki kuwa har da Iran da Saudi Arabia sun shiga yaki, batun da ya sanya manazarta ke kallonsa a matsayin yaki na akida tsakanin mabiya Sunni da 'yan Shi'a, duba da irin tsamin dangantakar da ke tsakanin Saudiyya da Iran.

Wani lamari da ya sauya alkiblar yakin na Siriya, shi ne shiga yakin da 'yan kungyiar 'yan ta'adda da aka yi lakabi IS suka yi, cikin shekarar 2014 har ma suka kai ga karbe iko da garuruwa da dama da nufin girka daular Islama. Ko da dai wasu daga cikinsu sun bar hannusu bayan da mayaka na kungiyar Kurdawa suka afka musu. Shigar IS din yakin na Siriya ya sanya kasashen yamma dake marawa 'yan tawaye baya suka girka wani kawace na yakar IS, yayin da kasar Rasha mai dafawa shugaba Assad ita shekara guda bayan shigan kawancen kasashen Yamma ita ma ta tura dakaru Siriya. Ko da yake kasashen Yamma dake marawa 'yan tawayen, suna kallon wannan yunkuri na Rasha a matsayin wata hanya ta murkushe masu adawa da gwamnati ne ba yakar IS ba.

Yakin dai ya jawo zub da jinin da duniya ta jima ba ta ga irinsa ba kamar yadda sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya bayyana.

Ya ce "halin da ake ciki a Siyasa matsananci ne kuma bai da kyan gani. Rabon da duniya ta ga irin wannan bala'i tun lokacin da aka yi yakin duniya na biyu"

Halin da aka shiga dai ya sanya zama na sulhu a lokuta da dama wanda ba su tsinanan komai ba. Sai dai na baya-bayan da aka yi a cikin watan jiya ya haifar da da mai ido, wanda ya yi sanadin kaiwa ga tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke rikici da juna. Har aka samu sukunin kai kayan agaji ga masu bukata, sai dai yakin na Siriya ya barwa dunyia tabon da ba za ta manta da shi, idan aka yi la'akari da yadda 'yan gudun hijira suka yi ta turuwa zuwa kasahsen duniya musamman ma dai Turai.

Idomeni Flussüberquerung Flüchtlinge Mazedonien
Hoto: DW/D.Tosidis
Türkei Wladimir Putin und Barack Obama in Antalya
Hoto: picture alliance/AP Images/K. Ozer