1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru biyu da fara yakin Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 27, 2017

Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa rayuwar kanan yara sama da 500.000 na cikin hadari a Yemen.

https://p.dw.com/p/2a2ne
Kananan yara na cikin halin tasku a Yemen
Kananan yara na cikin halin tasku a YemenHoto: picture-alliance/Photoshot/M. Mohammed

Asusun na UNICEF ya bayyana hakan ne a dai-dai lokacin da ake cika shekaru biyu cif, da fara kai hare-haren taron dangi na kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiya a Yemen din, wanda ya haddasa matsalar rashin abinci mai gina jiki, da aka kiyasta yara akalla 462.000 na cikin halin tsaka mai wuya na yunwa da rashin ingantaccen abinci a sassa daban-daban na kasar. Sai dai a hannu guda mahukuntan Yemen din na gudanar da shagulgula na cika shekaru biyu da fara hare-haren na Saudiya da kawayenta. A jawabin da ya yi yayin da suke shagalin cika shekaru biyu na wannan gumurzu, Hadi Adnan Alkaf mataimakin gwamnan birnin Aden da ke hannun gwamnatin Shugaba Abedrabbo Mansour yaba wa ya yi da irin taimakon da suke samu daga Saudiyan da kawayenta yana mai cewa:

"Muna yin shagali domin nuna godiyarmu ga rundunar taron dangi da suka kawo dauki ga Shugaba Abedrabbo Mansour Hadi domin taimakonsa ya yaki 'yan tawayen Houthi da kuma magoya bayan tsohon Shugaba Ali Abdullah Saleh."