1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru goma da kisan Yitzhak Rabin

Mohammad Nasiru AwalNovember 4, 2005

Wai shin ina aka kwana a shirin wanzar da zaman lafiyar Gabas Ta Tsakiya shekaru goma bayan kisan na tsohon Firaministan na Isra´ila?

https://p.dw.com/p/Bu4S
Marigayi Yitzhak Rabin
Marigayi Yitzhak RabinHoto: AP

Jama´a ta hadu a dandalin sarakunan Isra´ila dake birnin Tel Aviv yammacin asabar bayan hutun Yahudawa, don nuna goyon baya ga shirin wanzar da zaman lafiya da Falasdinawa. An saurari jawaban `yan siyasa sannan an rera wakar zaman lafiya mai taken Schir la Shalom.

Shekaru biyu baya wato 1993, Isra´ila da kungiyar PLO sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta birnin Oslo, amma aiwatar da ita ta fuskanci babban cikas saboda adawar da ´yan kishin kasa karkashin jagorancin shugaban jam´iyar Likud Binjamin Netanyahu tare goyon bayan yahudawa ´yan kakagida suka nuna. A garesu Yitzhak Rabin maci amanar kasar Bani Yahudu ne kuma kowane mataki aka dauka kansa ma daidai ne.

Bisa al´ada kuwa Rabin mai shekaru 73 ba mai son halartar bukukuwa ba ne kuma ba´a ma taba ganin shi a bainar jama´a yana waka ba, in ban da wannan rana da ake taron goyon bayan zaman lafiya da Falasdinawa. Duk da kamfen din kyamar sa da masu matsanancin ra´ayin kishin addinin Yahudu ke yi, mafi rinjayen ´yan Isra´ila na goya masa baya da cewa yayi namijin kokari bisa gagarumin matakin da ya dauka na yin sulhu da Larabawa makwabta.

Lokacin da zai hau mota bayan wannan gangami a birnin Tel Aviv sai aka ji karar harbin bindiga sau biyu kafin kace kwabo Rabin ya fadi kasa jina-jina. Duk kokarin da aka yi na ceto ransa bayan an hanzarta kai shi asibiti ya citura.

Nan take aka cafke wanda ya yi masa kisan gillar wato wani dalibin fannin aikin lauya mai suna Jigal Amir dan shekaru 25, kuma dan gani kasheni addinin Yahudu wanda ya ce ya shafe wata 10 yana tsara yadda zai kashe Rabin. Wannan dan ra´ayin rikaun ya ce ta haka ne kawai zai iya hana aiwatar da shirin wanzar da zaman lafiyar na birnin Oslo.

Duk da kin jinin Rabin din a Isra´ila a wancan lokaci ba wanda ya taba tunanin cewa za´a yi masa kisan gilla a bainar jama´a. Hatta shi kan shi kanshi Rabin bai taba yin wannan tunani, saboda haka ne ya ke kin sa irin falmarar da harsashi ba ya huda ta a duk lokacin da zai fita bainar jama´a.

Daya daga cikin mutanen da suka fara mika ta´aziyarsu shi ne shugaban Falasdinawa marigayi Yasser Arafat.

“Ina mika ta´aziya ta ga uwargidansa, iyalinsa, gwamnatin Isra´ila da kuma al´umar Isra´ila baki daya.”

A da Rabin ya kasance mai ra´ayin rikau dangane da rikicin yankin GTT amma daga baya ya dawo daga rakiyar wannan ra´ayi kuma ya zabi hanyar zaman lafiya, ko da yake cimma zaman lafiya ba aba ce mai sauki ba.

“Sanya hannu kan yarjejeniyar nan tsakanin Falasdinawa da Isra´ila ba abu ne mai sauki ba.”

In ban da kungiyoyi masu tsattsauran ra´ayi a Lebanon a duk fadin duniya an nuna kaduwa da kisan Rabin, musamman ganin cewa kisan daidai ya ke da share shirin zaman lafiyar gaba daya.

Yau dai shekaru 10 baya ya tabbata cewa an samu koma baya a shirin wanzar da zaman lafiya duk da dan ci-gaba da bai taka kara ya karya ba da aka samu wato kamar janyewar Isra´ila daga Zirin Gaza to amma har yanzu Falasdinawa ba su samu kasar kansu ba.