1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru shida da rikicin Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 15, 2017

Mutane da dama sun hallaka yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wasu hare-haren kunar bakin wake a Siriya.

https://p.dw.com/p/2ZDa0
Ci gaba da hare-haren ta'addanci a Siriya
Ci gaba da hare-haren ta'addanci a SiriyaHoto: picture alliance/Zumapress

Hare-haren dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da bangaren gwamnati da na 'yan adawa ke ci gaba da tattaunawar sulhu a Astana babban birnin kasar Kazakhstan. Sai dai an samu tsaiko na halaratar 'yan tawaye koda yake a yanzu sun bayyana cewa za su hallata. Tuni dai babban jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Siriyan Staffan de Mistura ya sanar da cewa shi kam ya gama zama a Astanan, bayan tattaunawa ta tsahon kwanaki biyu da wakilan kasashen Rasha da Iran ba tare da halartar 'yan tawayen ba. Shekaru shida ke nan dai da fara juyin-juya hali a Siriya da nufin kifar da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad wanda ya rikide zuwa yakin basasa, kana ya haddasa asarar dinbin rayukan al'umma da kuma tilasta wasu miliyoyi yin gudun hijira. Shugaba Assad dai na ci gaba da samun galaba a yakin na Siriya, abin da ya sanya masu fashin baki ke ganin cewa yakin ka iya kawo karshe bada jimawa.