1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shell zai tsayar da aiki a wani sashin Najeriya

Yusuf Bala Nayaya
March 7, 2017

Kanfanin ya dauki wannan mataki a lokacin da Najeriya ta ga halin tasku sakamakon faduwar darajar albarkatun mai a kasuwannin duniya da ma raguwar abin da kasar ke fitarwa a duk rana saboda ayyuka na 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/2Ylf9
Symbolbild Royal Dutch Shell Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/DW-Montage

Kamfanin hakar albarkatun man fetur a Najeriya Shell ya bayyana cewa zai rufe aikin hakar albarkatun a yankin hakar albarkatu a teku na Bonga saboda dalilai na yin gyara tsawon wata guda, abin da zai sanya a samu raguwar ganga 200,000 a kowace rana na albarkatun da kamfanin ke hakowa, lamarin kuma da ke zuwa bayan da kasar ta ga hali na tasku sakamakon faduwar darajar albarkatun na mai a kasuwannin duniya da ma raguwar abin da kasar ke fitarwa a duk rana saboda ayyuka na 'yan ta'adda masu fasa bututun mai a yankin Niger Delta.

Babban Manaja a kamfanin Bayo Ojulari ya ce aikin zai mayar da hankali a gyaran wurin ajiyar albarkatun na mai a babban jirginsu na Bonga da ke a kan teku. Wannan jirgi dai a inda aka girkeshi a teku ana iya hakar albarkatun mai da suka kai ganga 225,000 baya ga miliyoyi na ma'aunin iskar gas.

Wannan gyara dai na zuwa a daidai lokacin da Najeriya ke bukatar kari na yawan abin da ta ke fitarwa zuwa kasuwar duniya duba da matsi na tattalin arziki da kasar ta fiskanta, ga bukata ta kudade na kasashen waje.