1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

240309 Kosovo Völkerrecht

March 24, 2009

Waiwaye a game da yaƙin ƙarshe da ya faru a nahiyar Turai

https://p.dw.com/p/HIkS
Janar Klaus NaumannHoto: picture-alliance/dpa

Shekaru 10 da suka wuce, a rana mai kamar ta yau, wato 24 ga watan Maris,1999. Rundunar sojojin ƙungiyar NATO, ta kaɗɗamar da yaƙi na tsawon sati 11 akan dakarun sojin ƙasar Sabiya, domin su kare kisan ƙare dangin da aka tasamma yi wa ƙabilar Albaniyawa dake zaune a lardin Kosobo. Kuma an kaɗɗamar da yaƙin ne, bayan da yarjejeniyar zaman lafiya ta rushe, tsakanin gwamnatin tsohon shugaban Sabiya Slobodan Milosevic da kuma wakilan Albaniyawa dake lardin kosobo a kudancin ƙasar.

Shugabannin Nahiyar Turai sun yanke hukuncin afkawa dakarun Sabiyan da yaƙi ne a matsayin hanya ɗaya tilo da za ta magance yaƙin da ya ɓarke tsakanin dakarun sojojin Sabiyya da na Albaniyawan Kosobo da aka fi sani da KLA da masu goyon bayansu. Wannan dai shi ne karo na farko da dakarun NATO suka afkawa wata ƙasa a Nahiyar Turai.

Klaus Naumann, shi ne shugaban kwamitin soji na ƙungiyar NATO a lokacin da aka gudanar da yaƙin, ya kuma tuna yadda aka yanke wannan hukunci, bayan da aka shafe wata guda ana kai gwauro akai mari, wajen sasanta ɓangarorin da suke rikici da juna. Inda ya ce, a zahirin gaskiya sun yi ta ƙoƙarin sasanta ɓangarorin biyu, tun a watan Afrilun 1989, to amma a karshe sai suka tashi ba nauyi, sakamakon yadda dukkanin ɓangarorin suka zaɓi yin amfani da ƙarfi a matsayin hanyar da za a warware matsalar, idan har hakan ya zama dole. a ɗaya hannun kuma, ba su da wata dama da za su iya hana dakarun sojin kosobo masu adawar 'yanci, su shiga ɓangaren da Sabiyawa suka shata iyaka. a cewar sa, wannan ita ce gazawar su.


A nasa ɓagaren Joseph Marko, wanda masani ne akan shari'ar ƙasa da ƙasa, ya bayyana batun shiga tsakanin da NATO ta yi a Kosobo ta hanayar yaƙi, a matsayin gajiyawar ƙasashen duniya, to amma ya ƙara da cewa, a bin da ya faru a shekarar 1999, har yanzu ana kallon sa a matsayin wata hanyar kai ɗauki ta fuskar dokokin ƙasa da ƙasa. To sai dai har yanzu shi yana ganin da sauran rina a kaba.


Ƙungiyar NATO dai ta shafe kimanin kwanaki 78 tana gwabza yaƙi, kafin ta samu nasarar tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki, inda daga baya Majalisar Ɗinkin Duniya ta samu hurumin kafa sansanin tabbatar da zaman lafiya. Yaƙin dai da ya gudana tsakanin dakarun Sabiyan da Albaniyawan Kosobo, ya yi sanadiyar mutuwar dubun-dubatar Albaniyawa tare da ɗaiɗaicewar miliyoyi daga cikinsu, inda ya zuwa yanzu kimanin waɗanda suka koma gida, ba su wuce mutane 100,000 ba a tsawon shekaru 10.


Safiya Razkai, na ɗaya daga cikin Albaniyawan da ta rasa gabaɗayan 'ya'yanta, in ban da yaro ɗaya kacal da ya tsira, ta kuma bayyana cewa, a lokacin da suka koma gidajensu, sun tarar duk an ƙone gidajen, an kuma lalata komai. Dukkanin dabbobi da suka haɗa da tumaki da awaki da kuma karnuka duk anƙone su, wasu kuma an harbe su har lahira, babu wani abu da yai saura.


Har yanzu dai akwai sauran zaman ɗar-ɗar a wannan yanki na Sabiya da Kosobo, musamman ma dai daga lokacin da majalisar dokokin Kosobo ta ɓalle, ta kuma samu 'yancin kanta daga Sabiya, a watan Fabrairun Shekara ta 2008, 'yancin da ƙasashe fiye da 50 suka amince da shi, ciki har da Amirka da kuma kasashe mafiya yawa daga Ƙungiyar Tarayyar Turai.

Mawallafi: Fabian Schmidt / Abba Bashir

Edita: Yahouza Madobi