1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shige da fice tsakanin Birtaniya da EU

July 31, 2017

Birtaniya ta ce a karshen watan Maris na 2019 za ta kawo karshen shige da fice ba tare da shinge ba tsakaninta da kasashen kungiyar EU

https://p.dw.com/p/2hT6o
Belgien Brüssel EU-Gipfel Premierministerin Theresa May
Hoto: Reuters/F. Lenoir

 

Shige da fice ba tare da shamaki ba tsakanin kasashen kungiyar tarayyar Turai da Birtaniya za ta kawo karshe a watan Maris na 2019 lokacin da Birtaniya za ta fice daga cikin kungiyar EU kamar yadda mai magana da yawun Firaministar Birtaniya Theresa May ya sanar da hakan a ranar litinin din nan.

A makon da ya gabata ministan kudin Birtaniya Philip Hammond ya ce ba za'a sami wani sauyi a dokokin shige da fice ba idan Birtaniya ta fita kungiyar ta EU.

Mai magana da yawun Firaministar yace tuni gwamnatin Birtaniyar ta fara tsara cikakken jadawali kan hakkokin yan kungiyar tarayyar Turai bayan ficewar ta Birtaniya.

Duk da bayanai masu cin karo da juna daga manyan jami'an Theresa May kan shirin gwamnatin na ficewa daga kungiyar EU, mai magana da yawun Firaministar yace matsayin gwamnatin na nan yadda yake kamar yadda Firaministar ta sanar a watan Janairu.