1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin ƙasar Jamus ma tana da wani tsari na ba da agaji ga matalautan ƙasashe

Bashir, AbbaMay 13, 2008

Bayani game da tsarin ƙasar Jamus a kan batun bayar da tallafi ga ƙasashe masu tasowa

https://p.dw.com/p/DzGc
Tambarin shirin ba da agaji na ƙasar Jamus (DED)

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Faruku Baffa daga Jihar Zamfara a Najeriya; Malamin dai yana son ya san cewa, ko ƙasar Jamus ma tana da wani shiri na tallafin jinƙai kamar irin wanda Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki kan bayar?


Amsa: To ƙasar jamus dai ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da suka sami ci-gaba ta fuskar tattalin arziƙin ƙasa. kuma ita ce kan gaba wajen ba da tallafi ga ƙasashe masu tasowa a tsakanin dukkanin ƙasashen da suke da ci-gaban masana'antu. Domin kuwa ko a tsakanin shekarar 1991-1999 gwamnatin Jamus ta ware Euro na gugar Euro, har miliyan 5000 ga ofishin harkokin ƙasashen waje, domin amfani da su wujen bayar da tallafin jinkai ga ƙasasshe masu tasowa. A taƙaice dai bayanin jimilar abin da jamus ke keɓewa domin ayyukan jinkai ya ninka wannan adadi ninkin ba ninkin.


Haka kuma wani abu da ya kamata a sani shi ne cewa, gwamnatin ƙasar ta Jamus na bayar da tallafin ne, ta fuskoki daban-daban da suka haɗa da bayar da taimako kai tsaye ga gwamnatocin ƙasashen a matsayin bashi ko don jinkai, ko kuma ta hanun wasu ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa, kamar Majalisar Ɗinkin Duniya, Ƙungiyar Tarayyar Turai, da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu.


Tun bayan sake haɗewar Jamus waje guda, irin taimakon ci-gaba da ƙasar ke bayarwa ga ƙasashe masu tasowa ya fi mai da hankali ne ga gabashin Turai da kum ƙananan ƙasashen da suka sami ‘yanci daga tsohuwar Tarayyar Soviet, da nufin inganta rayuwar mutanen wannan yanki da kuma rage yawan kwarara zuwa yammacin Tarai. Bugu da ƙari yankin Gabas ta Tsakiya yana samun kulawa ta musamman a ƙoƙarin da Jamus ke yi na ganin ta kafa ginshiƙin zaman lafiya tare da ɗabbaƙa tattaunawar sulhu ko kuma fahimtar juna tsakanin ƙasashen Turai da na Musulmai.