1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin da gaske ne an samu zanen siffa mai kama da fuskar mutum a duniyar ...

Bashir, AbbaMay 19, 2008

Bayani game da binciken da masana suka yi akan duniyar Mars

https://p.dw.com/p/E2hd
Hoto mai kama da fuskar mutum a duniyar MarsHoto: AP

Tambaya: Shin wai da gaske ne an samu zanen siffa mai kama da fuskar mutum a duniyar  Mars? Da fatan za ku sanar da ni gaskiyar batu game da  binciken da masana suka yi akan duniyar Mars. Wannan ita ce tambayar da  muka samu daga hannun Malam Hassan Shugaba daga ƙasar Sudan.


Amsa: Gaskiya  akwai zanen sifffa ko halittu masu kama da ta mutane  a duniyar mars, domin kuwa wasu hotunan masu kama da na Indiyawan daji da aka  ɗauko a duniyar Mars, sun nuna zanen fuskokin wasu halittu masu kama da mutane. Ko da yake  hotunan da alamu kamar an ɗauke su ne a lokacin da rana ko dai ta fara fitowa ko kuma tana shirin faɗuwa, amma dai ya bayyana siffa ta fuskar bil'adama kwatankwacin irin alamun halittu da mukan gani ko hasashe a cikin  gajimare.


Duniyar Mars ita ce duniya ta huɗu  da ke kusa da  rana bayan duniyar ɗan Adam daga cikin duniyoyi tara kamar yadda masana ilimin  sararin samaniya suka bayyana. Kuma wannan suna nata ya samo asali ne daga  wani gunkin Romawa. Haka kuma baki ɗaya girman duniyar  Mars bai fi rabin girman  duniyar da mutane ke zaune a ciki ba, sai dai kuma cike take da duwatsu da kwazazzabai waɗanda suka kera wanda ake dasu a duniyar ɗan Adam.


To har'ila yau kuma kwana ɗaya a duniyar Mars ya fi na duniyar ɗanm Adam da awa 12. Wato kamar yadda kowa yasan cewa awa 24 suke kwana ɗaya a duniyarmu, ita duniyar Mars awa 36 kenan ke kwana ɗaya. Hakan ne kuma yasa  kwanaki 687 ne ke shekara guda a Mars, saɓanin kwanaki 365 a duniyar dan Adam.


Ikon Allah ba shi da iyaka, domin kuwa har'ila yau duniyar Mars  da akwai kwazazzabai da dama masu yanayi da wutsiyar koguna  to  sai dai a ƙafe suke sabo da tsananin sanyi wanda ke sa duk wani abu mai ruwa-ruwa  na wurin ya sandare.


To mai yiwuwa mutum ya yi tunani cewa saboda tsananin sanyin da ake batu wannan wuri na da shi, ƙila za a iya hura wuta a ji ɗimi. To ko kusa ba shi yiwuwa saboda binciken masana ya nunar da cewa, ba a samun makamashi a duniyar Mars, kuma babu nau'in iskar nan ta (Oxygen) a sararin samaniyarta. To ba ma wannan ba kaɗai, ko da mutum zai yi ƙoƙarin ɗaukar wani ɓangare na irin ƙanƙarar da ake samu a wanann duniya ya ce zai narka ta zuwa ruwa, ƙanƙarar za ta narke, to amma kuma mai makon ta zama ruwa sai ta zama iska duk dai sabo da rashin wasu sinadarai a sararin samaniyar duniyar Mars ɗin waɗanda za su ba da damar yin hakan.