1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin mene ne Dodo?

Yusuf BalaMarch 30, 2016

Kalmar ta Dodo dai ta rabu gida biyu akwai Dodo na sarari da Dodon boye wanda ake bayyana shi a cikin Tatsuniyar Hausa.

https://p.dw.com/p/1IK24
Graffiti einer Medusa auf einer Mauer
Sigar da Dodo ke bayyana a wani lokaciHoto: Fotolia/Zapatisthack

Dr. Tahir Adam (Baba Impossible) na Sashin Hausa a jami'ar Bayero da ke a Kano Najeriya ya yi karin haske a zantawa da DW.

Dr. Tahir Adam (Baba Impossible): Kalmar "Dodo" shi ne abin tsoro ko abin da ido ba ya iya gani ko ya sarrafa shi ko ya yi bayani, kafin zuwan Musulunci kasar Hausa aljanu ne ake bautawa su ne ubangiji.

Kalmar ta Dodo dai ta rabu gida biyu akwai Dodo na sarari da Dodon boye wanda ake bayyana shi a cikin Tatsuniyar Hausa, a nan sai kaga an sifanta Dodo da aljani abin tsoro wanda yakan iya sarrafa kansa ya cutar da dan Adam, shi kuwa na sarari duk wani abu da idan ido ya gani zai tsorata ko wata inuwa ko fatalwa ko wani abu da ake ba wa yara tsoro da shi, shi a ke kira da wannan kalma.

Galerie: Star Wars, Bild 3
Sigar da Dodo ke fita a bayan wata mataHoto: dpa

Me ya sa ake jin tsoron shi Dodo?

Dakta Tahir Adamu (Baba Impossible): To ai misali ana jin tsoron mutuwa ne saboda idan an mutu ba za a dawo ba, ana tsoron Dodo saboda zai iya kashe mutum ko ya cutar da shi ko ya sa wa mutum abin da ba zai ji ba dadi, wannan a bangaren babban mutum kenan, shi kuwa a bangaren yaro duk wani abu da za a iya shuna masa ya ba shi tsoro alal misali kunkuniya ko a dauki auduga da zarar an nuna masa sai ya rika jin tsoro wato dai ita wannan kalma ta Dodo duk wani abu da zai bada tsoro wanda kuma ido ba ya iya tabbatar da shi, amma abin da ka sani karara ba a kiransa da sunan Dodo, kamar misali mutuwa tun da an san da za ta zo ta dauki mutum ta tafi, amma duk abin da yake a boye zai iya zuwa ya illata mutum shi ake kira Dodo.

Ko shin akwai wani shashi na duniya da za a ce nan ne Dodanni suka fi yawa?

Dakta Tahir Adamu (Baba Impossible): A a ko'ina al'umma suke a duniya suna da irin nasu Dodo, domun zaka ga alal misali a kowane yanki zaka ga suna da irin abubuwa kamar fatalwa da dai dai sauransu. Dan haka kowa da akwai irin abin da suke dauka su yi amfani da shi dan bada tsoro.