1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin ta yaya dabbobin cikin teku suke iya gani a ruwa

Abba BashirMay 7, 2007

Bayanin yadda dabbobi mazauna Teku suke samun kyakkyawan gani a karkashin ruwa

https://p.dw.com/p/BvUp
Idon wata dabbar Ruwa
Idon wata dabbar RuwaHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Abdullahi: Tambaya ta gaba ta fito daga Hannun Malam Jilani Aminu daga Jihar Katsinan tarayyar Najeriya; Malamin cewa yayi, Kota yaya dabbobi mazauna cikin teku suke iya samun kyakkyawan gani a karkashin Ruwa?

Bashir: Gani halittace daga cikin halittun da Al-khaliku ya albarkaci mutane da dabbobi dasu.Ga mafi yawan dabbobin dake ruwa, gani abu ne mai muhimmanci kwarai da gaske, saboda farauta da kuma tsaron kai. Haka kuma, suna dauke da ido wanda aka yi musu na musamman saboda zama a ruwa.

Abdullahi: To ta yaya dabbobin ruwa suke samun damar gani sosai a cikin ruwa?

Bashir: To a karkashin, dammar da ake da ita ta gani,tana raguwa akai-akai yayin da aka dada nutsawa cikin ruwa sosai, musamman ma idan an wuce nisan mitoci 30, sabodahaka halittun da suke rayuwa a cikin wannan zurfi na ruwa, wanda ya wuce mita 30n, an halitta musu idanuwa na musamman da suka dace da rayuwarsu a wannan wuri.

Abdullahi: To hakan yana nuna kenan akwai banbanci na halittar Ido tsakanin halittun cikin Ruwa da kuma na doron kasa?

Bashir: To dama dai,Dabbobin ruwa, ba kamar dabbobi masu rayuwa a doron kasa suke ba ,su dabbobin ruwa, kwayar idonsu na dauke da makaran da suke hana ruwa shiga idonsu kuma su biya musu dukkan bukatunsu na zaman ruwa. Idan kuwa aka kwatanta idanunsu dana dabbobin doron kasa kasa, nasu yana da fadi (wato ma’ana kwayar idonsu); kuma yana taimaka musu wajen ganin abu komai nisansa kuwa sai su ganshi a kusa. Idan suka ga abu daga wuri mai nisa, sai kwayar idon ta koma ciki tare da taimakon wasu gabbai na musamman a cikin idon, sai suga girmansa kuma su gane ko menene.

Abdullahi: Wane daliline yasa idanun nasu suke da wadannan siffofi?

Dalilin da yasa idonsu yake da irin wannan sifa; shine yadda hasken da suke gani dashi yake watsuwa a Ruwa. Sabodahaka kwayar idon halittun ruwa , misali ace kifi,ba kamar ta Dan-adam bace da baya iya gani sosai a cikin ruwa.

Abdullahi: To abin haka yake har ga masu manya-manyan ido irin su kunamar-ruwa wato (Octopus) a turance?

Bashir: E- to ga halittu kamar su kunamar ruwa masu manyan idanu, anyi mata wadannan idanu ne domin su cike gurbin rashin kyakkyawan hasken dake can karkashin ruwa. Hakazalika kifi mai manyan Idanu idan yayi nutso kasa da mitoci 300, yana bukatar ya riski hasken gabansa kafin ya gane abinda ke gabansa, sabodahaka suna da wasu halittu na Ji, masu amfani da kadawar hasken shudin launi dake fitowa a cikin ruwa. Saboda wannan ne, yasa akwai tulin irin wadannan haske a jikin idanunsu.

Abdullahi: Ko wane darasi ya kamata al’umma su koya , dangane da tsarin Idon halittun cikin Ruwa?

Bashir: To Kamar yadda aka fahimta daga wadannan misalai, kowance halitta mai rai ,tana da idanu irinnata, wadanda aka halitta musamman ta yadda zasu da irin bukatunta. Wannan hujja itace ta tabbatar mana da cewa, duk halittarsu aka yi kamar yadda suke daga mahalicci mai wanzajjiyar hikima. Ilmi da kasaitar iko.Wato Allah Mahaliccin komai.