1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin ƙuri'ar raba gardama a Sudan

October 5, 2010

A ƙasar Sudan ana ci gaba da shirye-shiryen kaɗa ƙuri'ar raba gardama game da makomar kudancin ƙasar.

https://p.dw.com/p/PVjL
Jami'an tsaro a cikin ɗamara a kudancin SudanHoto: AP

A wannan makon dai halin da ake ciki a ƙasar Sudan dangane da hada-hadar bai wa kudancin ƙasar cikakken ikon cin gashin kai shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus, inda jaridar Financial Times Deutschland ta ce ministan harkokin waje Guido Westerwelle na hangen rikici a ƙasar Sudan kuma ya bayyana shirinsa na taimakawa wajen ganin kome ya tafi salin-alin a cikin lumana..Sai dai kuma jaridar ta ci gaba da cewa:

"A dai halin da ake ciki yanzun akwai masu hasashen ɓillar wani rikicin da zai kasance mafi muni akan na Somaliya. Daga cikin masu irin wannan hasashe kuwa har da Meles Zenawi na ƙasar Habasha, wanda ya ce a karon farko a cikin shekaru ashirin da suka wuce za a ƙirƙiro wata sabuwar ƙasa a Afirka a yankin ƙasar Sudan kuma shugaba Omar Al-Bashir shi ne zai tashi a tutar babu. Ta la'akari da haka mai yiwuwa a fuskanci wani yaƙi na basasa domin hana wannan ɓallewa. Domin kuwa ita ma ƙungiyar 'yantar da kudancin Sudan ta SPLM ta ce faufau ba zata yarda a ci gaba da ƙwararsu a manufofi na ƙasa baki ɗaya ba."

Sudan Demonstrationen
Zanga-zangar neman canji a SudanHoto: AP

Ita kuwa mujallar Stiftung Wissenschaft und Politik cewa tayi a taƙaice:

"A halin yanzu haka dai hankali gaba ɗaya ya karkata ne zuwa ga abin da zai biyo bayan ƙuri'ar raba gardamar da aka shirya gudanarwa dangane da makomar kudancin Sudan a ranar tara ga watan janairun shekara ta 2011."

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta tofa albarkacin bakinta akan matsalar ta Sudan a cikin wani rahoton da ta bayar ƙarƙashin taken:"Naƙuda mai raɗadin gaske a fafutukar samar da wata ƙasa." Jaridar ta ce:

"Tuni dai unguwannin zoma suka fara jan ɗamara, inda suke gabatar da jawabai iri daban-daban, galibi don ba da ƙwarin guiwa bisa manufa. Amma fa hakan ba zata iya kawar da hankali da babban haɗarin dake tafe ba. Haifuwar wata ƙasa a kudancin Sudan ba zata tafi salin alin ba tare da wata tangarɗa ba."

A wannan makon aka gabatar da shari'a akan tsofon kukun Usama Bin Ladin a birnin New York na ƙasar Amirka. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

"Bisa ga dukkannin alamu dai Ahmad Khalfan Ghailani, ɗan usulin tsuburin Zanzibar da ake zarginsa da hannu a hare-haren da aka kai kan ofisoshin jakadancin Amirka a Kenya da Tanzaniya a shekara ta 1998 tare da sanadiyyar rayukan mutane metan da ashirin da huɗu zai fiskanci hukunci ne na kisa. Ghailani, wanda aka ɗauko shi daga sansanin gwale-gwale na Guantanamo, tuni ya sanar ta bakin lauyansa cewar ba ya da wani laifi."

Tattalin arziƙin gabacin Kongo na fuskantar barazanar taɓarɓarewa kwata-kwata sakamakon haramta dukkan ayyukan haƙan ma'adinai da gwamnati ta yi a cewar jaridar Die Tageszeitung. Jaridar ta ce:

Coltan aussortierung von Hand im Kongo
Gwamnati ta dakatar da haƙan ma'adinai a KongoHoto: BGR

"Dalilin da gwamnati ta bayar a game da dokar ta haramci shi ne kasancewar ƙungiyoyin 'yan bindiga na amfani da waɗannan ma'adinai don ci gaba da ƙarfafa matsayinsu a wannan yanki kuma a saboda haka dokar ta shafi dukkan masu aikin haƙan ma'adinai kama daga ƙanana zuwa manyan kamfanoni a gabacin Kongo."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu