1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Amurka na dasa na´ura a nahiyar Turai

March 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuP8

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gargadi kasashen turai, da kada su sake shirin Amurka na dasa na´urar kade makami mai linzami, a wasu kasashen nahiyar ya rarraba yayan kungiyyar ta Eu.

Merkel taci gaba da cewa ,abu ne wajibi yayan kungiyyar na Eu su zama tsintsiya daya madaurin ki guda, game da matsayin su akan wannan batu.

To, sai dai a waje daya, wasu daga cikin yan jam´iyyar CDU ta shugaba Merkel, musanmamma tsohon ministan tsaron kasar, wato Volker Rühe, na da ra´ayi ne na adawa da wannan shiri.

A cewar masu adawa da shirin , kamata yayi a tuntubi kasar Russia kafin amincewa da wannan shiri na Amurka.

Tuni dai mahukuntan na Mosco suka yi Allah wadai da wannan shiri, da Amurka tace zata yi shine da nufin zama cikin shiri, ga duk wata barazana daka zo mata daga Iran.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa kasar ta Amurka na shirin dasa wannan na´ura ce a kasashen Poland da kuma kasar Czech.