1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SHIRIN BA DA TAIMAKON RAYA KASA NA JAMUS YA SHIGA KAMFAR TALLAFI

Yahaya AhmedNovember 27, 2003
https://p.dw.com/p/BvnO
Kungiyoyin Welthungerhilfe da Terre des hommes, sun yi suka ga yadda a hankali gwamnatin tarayya ke nakuda da batutuwan da suka shafi ba da taimamkon raya kasashe. A wani taron maneman labaran da suka kira a birnin Berlin, don gabatad da rahotonsu na wannan shekarar, wanda kuma shi ne na karo na 11 a jere, kungiyoyin sun bayyana cewa, kudin da gwamnatin tarayya ta ware a shekarar bara, ga asusun ba da taimakon raya kasashe, bai zarce kashi sifili da digo 27 cikin dari na kudaden shiganta a wànnán shekarar ba. A shekaru biyun da suka wuce ma, haka lamarin ya kasance, saboda kamfar tallafin da asusun ba ta taimakon raya kasashe na Jamus ya shiga, sakamakon nàwár da gwamnatin tarayya ke yi wajen ba da isashen taimakon ku#a#e. A halin yanzu kuma, babu wata alamar da ke nuna cewa, za a sami wani sauyi a wannan salon, inji Peter Mucke, wani dan kwamitin shugabancin kungiyar Terre des hommes. Ya kara da cewa:- "Gwamnatin tarayya tana ci gaba da nisanta kanta, daga gurin da ta sanya a gaba, a fannin ba da taimakon raya kasashe. Hakan kuwa zai sa mutuncinta da kuma manufofin siyasarta dusashewa. Ko da ma ta kai ga ba da kashi sifili da digo 33 cikin dari na kudaden shiganta a shekara ta 2006, kamar yadda ta yi alkawari, ta kuma ci gaba da yin kari a duk shekara, ba za ta cim ma gurin kashi sifili da digo 7 cikin dari, da majalisar dinkin Duniya ta amince da shi ba, sai bayan shekara ta 2043." Peter Muck ya ba da misalan wasu Kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai, kamarsu Ireland, da Faransa da Belgium, wadanda suke kan hanyar cim ma gurin ba da taimakon raya kasa na kashi sifili da digo 33 cikin dari, kafin shekara ta 2006. A nasa ganin, Jamus ba za ta iya cim ma wannan gurin ba. A cikin nasa jawabin, babban sakataren kungiyar Deutsche Welthungerhilfe, Hans-Joachim Preuß, ya yabi irin kwazon da ministan ba da taimakon raya kasashe, Heidemarie Wiezorek-Zeul ke nunawa a majalisar ministocin tarayya. Amma duk da haka, ba a sami wani muhimmin sakamako a huskar kasafin kudin ma'aikatar ba, abin da kuma ke kara raunana yunkurin da ake yi na yakan talauci a duniya. Hans Joachim-Preuß, ya kara da cewa:- "Gaba daya dai, duk inda aka waiwaya a fannin samar wa jama'a muhimman ababan rayuwa na yau da kullum, kamarsu ilimi, da kiwon lafiya, ko samad da ruwan sha mai tsabta, sai a ga cewa, a cikin shekarun da suka wuce, an sami koma baya a hidimomin da ake yi." Duk da matsin tattalin arzikin da Jamus ke huskanta dai, kungiyoyin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara tallafin da take bayarwa, wajen yakan talauci a duniya. Kazalika kuma sun nuna damuwarsu ga habakar yaduwar cutar nan ta AIDS, inda suka nanata cewa, daga cikin mutane miliyan 42 da aka yi kiyasin sun kamu da cutar a duniya baki daya, kusan miliyan 30 ne ke zaune a Afirka. Game da hakan ne kuwa suka bukaci gwamnatin Jamus da ta yi amfani da angizon da take da shi, wajen shawo kan cibiyoyin bincike su kara ba da kaimi a binciken da suke gudanarwa don samad da magungunan warkad da cutar, kuma masu saukin farashi.