1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin binne Ford

December 31, 2006
https://p.dw.com/p/BuVy

A birnin Washinton din kasar Amurka,yan majalisar dokoki sun fara hallara domin janaizar tsohon shugaba Gerald Ford na Amurka.Mataimakin shugaban kasa Dick Cheney,a jawabinsa a wajen,ya yabawa marigayin adangane da ceto Amurka adaidai lokacin da ta kasance cikin mawuyacin hali.Mr Ford wanda ya kasance dan jammiyar Republican ,kuma dan majalisa na tsawon shekaru 25, ya shugabanci Amurka daga 1974-1977.Shine mutuzmin daya gaji tsohon shugaban Amurka Richard Nixon,wanda yayi murabus daga mulki sakamakon rikicin Watergate,.A ranar talatar data gabata nedai Mr Ford ya mutu,a shekaru 93 da haihuwa.Zaa binne shi ne a Machigan,a ranar larabar wannan makon.