1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin dakile fitinar yan ta´adda a Jamus

May 9, 2007
https://p.dw.com/p/BuLl

Mahukunta a Jamus sun kaddamar da tsattsauran shiri na sintirin dakile fitinar ta´addanci a jihohi shida dake kasar.

Rahotanni dai sun rawaito cewa ko da a yau, sai da jami´an suka kai ziyarar ba zata, izuwa wasu gurare 40 dake cikin wadannan jihohi.

A lokacin wannan sintiri dai yan sandan na kai hare hare ne a matsugunai da suke zargi maboyar masu tsattsauran ra´ayi ne dake da alaka da kungiyoyin yan ta´adda.

Bayanai dai sun nunar da cewa daukar wannan mataki, yazo ne a matsayin rgakafi na taron shugabannin kasashe 8 masu karfin masana´antu da ake shirin yi a garin Heiligendamm, dake nan Jamus ne.