1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin gangamin yan adawa a Nigeria

May 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuMT

Gabannin gudanar da zanga zanaga na lumana a fadin tarayyar Nigeria a yau,kungiyoyin maaikata da masu zaman kansu sun bayyana tsoronsu dangane da yiwuwar amfani da wannan dama wajen tozartawa jamaa a bangaren jamian tsaron kasar.Manyan kungiyoyin kwadago na kasar da jammiiyun adawa a Nigeriayar dai sun kira zanga zangar lumana na kasa baki daya a yau,bayan da hukumar zabe mai kanta a ta sanar da Umaru Musa yar Adua a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa daya gudana ranar 21 ga watan Afrilun daya gabata,zaben da masu gani da ido sukace an tabka magudi.

Shugabar daya daga cikin manyan kungiyoyi na sa ido a zaben ,Mabel Adinga Ade,ta sanar dacewa jamian leken asiri sun cafke daya daga cikin masu shirya wannan gangamin a Abuja,ayayinda sauran suka sami sakonnin gargadi. Specta General na yansanda a Nigeria Sunday Ehindero dai ya sanar dacewa zaa amince da gudanar da gangami a wasu yankunan kasar,sai dai duk wanda ya gudanar da hakan ba tare da izini ba zai fuskanci fushin yansandan.