Shirin kafa gwamnati a palasdinu
March 16, 2006Talla
MIDEAST
A yau ne ake kyautata zaton cewa,Kungiyar masu tsattsauran raayi na Hamas zata amince da batun nadin sabuwar gwamnati a yankin palasdinu,Sai dai bisa dukkan alamu tsohuwar jammiyar mulki ta fata bazata kasance cikin wannan gwamnati ba.
Kakakin yan Hamas dake yankin Salah al-Bardawil ya fadawa manema labaru hakan ayau ,bisa ga umurnin shugaba Mahmud Abbas,Abu mazen.Yace tun a daren jiya ne suka mikawa sauran kungiyoyi sabbin sauye sauye da aka samu.kuma an saurararon martaninsu a yau.
Ya kara dacewa idan sun amince da shiga gwamnatin hadakan,saanan zaa rarraba mukaman ministoci.
Majiysar yan Hamas din dai na nuni dacewa a yau ne kungiyar take jiran sakamakon tattauznawa na karshe dake gudana tsakanin shugabannin jammiyun siyasar yankin.