1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin kafa gwamnatin tarayya a Jamus na huskantar cikas.

YAHAYA AHMEDNovember 2, 2005

Yanayin siyasa da ake ciki yanzu a tarayyar Jamus na huskantar wata barazana, ta wargajewar shawarwarin da ake yi na kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakanin jam'iyyun CDU da SPD. Hakan kuwa ya zo ne bayan shugaban jam'iyyar SPD, Franz Münterfering, ya ba da sanarwar yin murabus daga mukaminsa. A daya bangaren kuma, shugaban jam'iyyar CSU, kuma Firamiyan jihar Baveriya, Edmond Stoiber, shi ma ya ce ba zai shiga sabuwar gwamnatin da za a kafan ba, inda aka tanadi ba shi mukamin ministan tattalin arziki na tarayya.

https://p.dw.com/p/Bu4V
Franz Münterfering, shugaban SPD, wanda murabus dinsa ke barazanar janyo wargajewar shawarwarin kafa gwamnatin tarayya.
Franz Münterfering, shugaban SPD, wanda murabus dinsa ke barazanar janyo wargajewar shawarwarin kafa gwamnatin tarayya.Hoto: dpa

Yunkurin kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa da ake yi a nan Jamus dai na huskantar wata barazana ta wargejewa a halin yanzu. Tun farkon wannan shekarar ne al’amura suka fara tabarbarewa a fagen siyasar tarayya, inda jam’iyyun adawa ke yi wa shirye-shiryen gwamnati babakere a majalisar dokoki. Kololuwar wannan ki-ki kaka din dai, ita ce lokacin zaben jihar Nord-Rheinwestfalia a cikin watan Mayun da ya gabata, inda jam’iyyar SPD, wadda ke jan ragamar mulkin jihar tun fiye da shekaru 30 da suka wuce, ta sha gagarumin kaye. Wannan sakamakon dai, ya sa jam’iyyar shugaba Schröder ta SPD ba ta da rinjayi kuma a majalisar dattijai ta Bundesrat. Hakan kuma ya kara karfafa wa jam’iyyun adawan gwiwa, wajen yi wa duk shirye-shiryen gwamnatin da za a gabatar wa majalisar dattijan, babakere.

Ganin hakan ne kuwa, ya sa shugaba Schröder, kiran zabe a cikin watan Satumba, shekara daya kafin cikar wa’adinsa. Ba a dai sami wata jam’iyyar da ta lashe wannan zaben da cikakken rinjayi ba. Sabili da haka ne aka shiga tattaunawa tsakanin jam’iyyun wajen kafa gwamnatin hadin gwiwa. Bayan shwarwarin da suka dade suna yi ne, jam’iyyun SPD da na CDU ne suka yarje kan kafa sabuwar gwamnatin ta gambiza.

Tun da aka shiga tattaunawa kan manufofin da sabuwar gwamnatin za ta sanya a gaba da kuma rarraba madafan iko ne, aka yi ta samun rashin jituwa tsakanin jam’iyyun. To a ran litinin nan ne kuma, ba zato ba tsammani, shugaban jam’iyyar SPD Franz Müntefering ya ba da sanarwar yin murabus daga mukaminsa, saboda rashin jituwar da aka samu tsakanin magoya bayansa wajen zaban sakatare-janar na jam’iyyar da kuma masu adawa da shi. A karshe dai, ’yar takarar masu adawar ne ta lashe zaben sakatare-janar din, abin da kuma ya bata wa Müntefering rai har kuma ya yanke shawarar yin Murabus.

Kwatsam sai ga shi kuma, shugaban jam’iyyar CSU kuma Firamiyan jihar Baveriya, Edmond Stoiber, shi ma ya bullo da nasa, inda ya bayyana cewa, ba zai rike mukamin ministan tattalin arzikin tarayya da aka tanadi ba shi a sabuwar gwamnatin da za a kafa ba. Ya fi gwammacewa ya saura a birnin Münich a mukaminsa na Firamiyan jihar Baveriyan, da ya taso zuwa birnin Berlin.

A halin yanzu dai, masharhanta kan harkokin siyasar Jamus, sun yarje kan cewa, ana cikin wani hali na rudami a fagen siyasar kasar nan, wanda ba a taba shiga ba tun kafa Jumhuriyar Tarayyar Jamus a shekarar 1949.

A jam’iyyun SPD da CSU din dai, sauran `ya`yan jam’iyyar sun rasa inda za su nufa. Tsoffin shugabanninsu kamar Theo Waigel, na CSU, sun fara yin kakkausar suka ga magadansu na yanzu. Shi dai Wigel, wanda a da shi ne ministan kudi na tarayya a gwamnatin Helmut Kohl, ya zargi Firamiyan jihar Baveriya Edmond Stoiber ne da cewa, ba shi da kishin jam’iyyar. Game da janyewar Firamiyan daga sabuwar gwamnatin, takwaran aikinsa na jihar Nord-Rheinwestfalen, Jürgen Rütgers na jam’iyyar CDU, ya bayyana cewa:-

„Ban fahimci Edmond Stoiber ba, da ya ke cewa, yana son samun cikakken bayani kan ginshikin da sabuwar gwamnatin za ta dogara a kai, kafin ya amince da ita. Ai shi da kansa ma, akwai gudummuwar da zai iya bayarwa a nan Berlin.“

Har ila yau dai, ana rade-radi kan dalilan da suka sanya Stoiber yanke shawarar ficewa daga sabuwar gwamnatin tun ma kafin ta kafu a hukumance. Kawo yanzu dai, cewa ya yi, al’amura sun sake masa, tun da Franz Münterefring ya yi murabus. Amma wasu masharhanta na ganin cewa, rashin jituwa tsakaninsa da shugaban jam’iyyar CDU Angela Merkel, wadda ita ce dai a halin yanzu, idan kome ya tafi daidai kamar yadda aka tsara, za ta shugabanci gwamnatin, na daya daga cikin muhimman dalilan da suka sa ya janye.

To ko ina kuma aka nufa daga nan ?

Ita dai Angela Merkel, wadda za ta kasance farkon shugaba mace ta gwamnatin tarayyar Jamus, ta dage kan bakanta na cewa:-

„A nawa ganin dai, kowa na sha’awar ganin an kafa wannan gwamnatin ta gambiza.“

Amma, abin tamabaya a nan shi ne, wai shugaban mai jiran gado, za ta iya magance wannan matsalar da cike gibin da Franz Müntefering da Edmond Stoiber suka bari kuwa ?