1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

shirin kyautata rayuwar matasa a Senegal

Zainab A MohammadDecember 26, 2005
https://p.dw.com/p/Bu32
Shugaba Abbdoulaye Wade na Senegal
Shugaba Abbdoulaye Wade na SenegalHoto: AP

Sama da watanni uku bayan an dawar dashi ta hanyar tilas daga moroko,Mamdou Diop mai shekaru 28 da haihuwa,har yanzu yana cikin bakin ciki da takaicin azabar daya fuskanta a yunkurinsa na zuwa turai ta barauniyar hanya.

Wannan bawan Allah dai ya kasance daya daga cikin dubban mutane dake kokarin kutsawa turai ta barauniyar hanyan nan na tsibran Ceuta da Mellila dake kan iyakar moroko,kuma ke karkashin tsaron kasar Spain.A watan satumban daya gabata kasashen biyu sun fuskaci matsalar daruruwan bakin haure yan Afrika dake kokarin shiga turai da zummar fara sabuwar rayuwa.

Kafofin yada labaru na duniya dai sun yayata hotunan wadannan yan Afrika da irin azabar da suka fuskata akokarinsu na tsallake shingen tsaro mai tsini da aka gindaya a wadannasn tsibrai biyu.asakamakon haska ne 14 daga cikinsu suka rasa rayukansu.Mafi yawa daga cikin bakin hauren kuwa sun fit one daga Senegal da Mali da Ghana da Guinea da kuma Nigeria.

Daya bayyana irin halin da suka tsinci kansu ciki,Ousmane Ngom, yace yan fasa kwaurin mutane dake kan iyakokin Spain da Morokk da suka amince dasu,sun kaisu na ne sun zubar dasu,inda suka rasa wani zabi face kutsawa da tilas ko kuma su komo gida su zame abun dariya.

A yanzu haka dai Ngom ya komo kashe kashen kaya tread dayakeyi a bakin kasuwar Sandaga dake birnin Dakar.Wannan mutumin wanda ya bar Senegal shekaru 6 da suka gabata domin hadewa day an uwanshi dake Italy,ya komo gida ba tare da ko sisi a jikinsa ba ,a wani jirgin sama na musamman da gwamnatin Moroko ta dauki hayansa a ranar 10 ga watan Octoba.

Daga cikin wadanda aka komo dasu ta wannan hanya dai akawa yan kasar ta Senegal 1,121 a jirage 8,day an mali 1,135 a jirage 7,dayan Yan Gambia 60 da yan Guine 93 da yan kamaru 129,day an Burkina faso 2 da yan Nigeria 2,inji maaikatar harkokin cikin gida na moroko.

Koran baki yan kasar Senegal daga Moroko ya sanya gwamnatin Dakar ta kaddamar da wani shirin komawa gona wa wadanda aka komo dasu din.

Akarkashin wanna shirin dai,kowane mutum guda zai samu dala dubu 7 ,daga lokacin shuka zuwa sayar da amfanin gona bayan girbi,wanda zai dauki tsawon watannin shida.

A yabzu haka dai gwamnatin Senegal na kokarin kamala shirin kaddamar da wannan tsari da kuma yiwuwan aiwatar dashi.Ayayinda a daya hannun kuma manazarta na shakkun cimma nasar aiwatar dasgi,kasancewar wadannan matsa sun rigaya sun leka sunga hasken duniyan turai,tayaya zasu amince da komawa filayen gonaki dauke da fatanya a sunan noma?

Ministan harkokin noma da albarkatun ruwa na kasar Habib Sy,yace wannan shirin nada nufin bawa matasan makaman dogaro ga kai ta halaltacciyar hanya,tare da cimma burin gwamnati na inganta harkokin noma.

Yace akarkashin wannan shirin,zaa rarraba matasan zuwa kungiyoyi 50.Kowace kungiya zata samu hectocin filin noma 100,tare da kayayyakin noma.A shekarar farko na wannan shírin zaa rarraba musu takin zamani da irin da zasu shuka.

Bugu da kari akwai kwararru daga faransa da zasa taimaka wajen horar dasu,kana zaa bawa kowace kungiya babura 2 ,domin saukaka musu harkokin sufuri.

Anadai kyautata zaton kaddamar rukunin farko na wannan shri a watan Disamban shekara mai zuwa.Daya gabatar tsarin shirin a watan Nuwamba,Ministan Harkokin Noman yace ,da wannan shirin bazasu nemi tallafin kudi ba saidai tallafin kwararru,kuma zasu nunawa kasashen turai da wadanda suka koro yan kasar tasu cewa, suna da madogara.

Dayake wadanda akayi wannan shirin basu san komai game da noma ba,gwamnati ta dauki nauyin kashe dala dubu 200 wajen horar dasu.

Itama Mali,wadda ke zama daya daga cikin kasashen Afrika data bayyana damuwanda dangane dakoran yan kasarta da Moroko tayi,ta kaddamar da wasu shirye shirye biyu na samarwa matasa ayyukanyi da tallafi.