1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin nukiliyar Iran da Kungiyar tarayyar

July 7, 2006
https://p.dw.com/p/BurO

ƙasar Iran ta ce a mako mai zuwa zata bada haske a matakin farko na martanin da zata bayar ga tayin Ihsani da ƙungiyar tarayyar turai ta gabatar mata. Jamiín ƙasar Iran dangane da shirin makamashin nukiliya Ali Larijani wanda ya gana da babban jamiín harkokin waje na ƙungiyar tarayyar turai Javier Solana a birnin Brussels, yace Iran na da nufin cigaba da shawarwari a game da batun nukiliyar. Shugaban hukumar makamashin nukiliya na majalisar dinkin duniya Mohammed el-Baradei ya ja hankalin Iran da cewa ƙasashen duniya sun fara kosawa saboda ƙin amincewar da ta yi na bayar da amsa ga tayin Ihsanin da aka yi mata idan ta dakatar da shirin ta na bunkasa sinadarin Uranium. Manyan ƙasashe masu faɗa aji na duniya na buƙatar Iran ta fayyace matsayin ta kafin taron G8 na ƙasashe masu cigaban masanaántu wanda zai gudana a birnin Mosco a ranar 15 ga watan Juli. Ministocin harkokin waje na ƙasashen Amurka da Rasha da China da Britaniya da Faransa da kuma Jamus zasu gudanar da taro a ranar Laraba mai zuwa domin shawarta matakin da zasu ɗauka a kan Iran idan bata bayar da amsa ga tayin Ihsanin ba kafin taron shugabannin na G8.