1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin rage sojin Amurka a Iraqi

April 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0R

Hukumar tsaron Amurka Pentagon ta ce akwai alamun rage yawan dakarun sojin Amurkan dake ƙasar Iraqi bisa samun nasarar kafa sabuwar haɗin ƙasa cikin hanzari. A hannu guda kuma, bayan ganawar su da sabon P/M da aka naɗa a Iraqi, Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice da sakataren tsaro Donald Rumsfeld, sun baiyana gamsuwa da kyakyawar aniyar da sabon P/M ke da ita na haɗa kan alúmar ƙasar Iraqi. Condoleezza Rice ta shaidawa manema labarai cewa sun gamsu matuƙa gaya, da sabon P/M Nuri al-Malik wanda ta baiyana da cewa mutum ne mai ƙwazo da hangen nesa. Shugaban ƙasar Amurka George W Bush wanda ya buƙaci kafa gwamnatin haɗin kan ƙasar a Bagadaza domin kawo ƙarshen zubar da jini a sakamakon tarzoma ta yan tawaye, ya tura manyan jamián biyu domin ganawa da sabon P/M Nuri al-Malik. Yawaitar tarzoma da tashe tashen hankula a Iraqin na dakushe karsashin Bush na fara janye sojojin Amurka daga Iraqi kafin zaben majalisun dokokin Amurka da zai gudana a cikin watan Nuwamba.