1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin shimfida demukiradiya a Iraki bai cimma manufa ba

August 3, 2006
https://p.dw.com/p/Buo0
Jakadan Birtaniya a Iraqi mai barin gado, William Patey yayi kashedi game da yiwuwar barkewar wani yakin basasa a Iraqin, wanda zai janyo rarrabuwar kasar. A cikin wasikarsa ta karshe da ya aikewa gwamnatin Birtaniya, jakadan ya ce yanzu an fi fuskantar barazanar fadawa wani yakin basasa gadan-gadan maimakon samun nasarar girke wata gwamnatin demukiradiyya a Iraqi. Mista Patey ya kara da cewa duk wani fata da shugaban Amirka GWB ke da shi na kafa wata gwamnati mai dorewa a Iraqin ya zama wani abin shakku. Wadannan kalaman na jakadan ya bambamta da matsayin gwamnatinsa a hukumance akan makomar Iraqi.