1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

shirin sulhu a uganda

Zainab A MohammedAugust 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5m

Hukumomin Uganda sun gindaya sharudda masu tsanani ,da zasu kasance sharan fagen cimma yarjejeniyar sulhu da kungiyar yan tawayen Lords Resistance Army ,inda ake bukatar mayakansu su hallara a sansanoni biyu ,akarkashin sa idanun wasu dakaru na daban.An dai gabatar da wadannan sharudda ne a yayin dakatar da zaman tattaunawa,da ake shirin gudanarwa a kudancin sudan,taronda a baya gwamnatin Ugandan tayi watsi batun tsagaita wuta da kungiyar yan adawan tayi ranar 4 ga watan Augusta.

Akarkashin gabatarwan gwamnatin Ugandan dai,zata dauki nauyin tafiyan mayakan adawan zuwa sansanonin biyu da ingantaccen tsaro ,tare sanya dakarun tsohuwar kungiyar yabn adawan Sudan ta SPLM,su kula dasu bayan sun isa sansanoni.Tuni dai kungiyar ta SPLM dake shiga tsakani ta amince da wannan shirin,a tattaunawar daya gudana a garin na Juba.To sai dai babu martini daga kungiyar yan tawayen LRA na Ugandan kawo yanzu.