1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin toshe shafukan sada zumunta a Kwango

Salissou Boukari
December 15, 2016

Hukumar sadarwa ta Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango ta nemi da kamfanonin wayar sadarwar kasar da su toshe shafukan sadarwa na zumunta daga ranar Lahadi mai zuwa.

https://p.dw.com/p/2UKcE
Äthiopien Addis Abeba Universität Kommunikation Internetsperre
Hoto: DW/J. Jeffrey

Yayin wani zaman taro da hukumar sadarwa ta kasar ta Kwango wato ARPTC ta gudanar tare da wakillan kamfanoni hudu na wayar sadarwa a kasar ta sanar da su wannan mataki. Hukumar sadarwar ta kuma ce, idan har daya daga cikin kamfanonin ya ki bin wannan umarni, to zai fuskanci fushinta, inda za ta kai a dakatar da izininsa na gudanar da ayyuka a kasar. Shafukan sadarwan da za a toshe sun hada da na Facebook, da WhatsApp, da Twitter da dai sauran su, inda za a dakatar da su a ranar Lahadi 18 ga watan Disamba daga bakin karfe 18 na yamma 'yan awoyi kafin karshen wa'adin mulkin Shugaba Kabila.