1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin yin sulhu a kasar Colombia

June 24, 2006
https://p.dw.com/p/Buso

A wani mataki na bazata, babbar kungiyar ´yan tawaye a Colombia wato FARC ta nuna shirin yin shawarwarin samar da zaman lafiya da gwamnati. To sai dai ta ce kafin a yi haka dole sai gwamnati ta janye dakarun tsaro daga lardunan Putamayo da Caquete dake kudancin kasar, inji kakakin kungiyar ta FARC Raul Reyes. Ban da haka kuma dole ne shugaba Alvaro Uribe ya rushe shirinsa na yaki da sojojin sari ka-noke. A lokacin da yake mayar da martani, wani kakakin gwamnati ya ce shugaba Uribe ba zai dakatar da yakin da ya daura da ´yan tawayen ba, hakazalika ba zai janye sojojin gwamnati daga wani yanki na kasar ba a matsayin wani sharadi na zama kan teburin shawarwari da ´yan tawayen. A halin da ake ciki kuwa daya kungiyar ´yan tawayen wadda ita ce ta biyu mafi girma a kasar wato ELN ta na tattauna batun samar da zaman lafiya da gwamnatin Kolumbia bisa wasu shawarwarin sulhu da kasar Kuba ta gabatar.