1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin zaben shugaban kasa a ranar 13 ga watan Nuwamba a Burkino Faso

Zainab A MohammadJune 20, 2005

Shugaba Blaise Compore na neman sake zarcewa a kan shugabanci a karo na uku

https://p.dw.com/p/BvbF
Hoto: AP

Jammiyar mulki ta kasar Burkino Faso watau CDP a takaice ta kamala wani taronta na kasa,inda ta sake zaban shugaba maici a yanzu ya sakeyin takara a zaben kasar dazai gudana karshen wannan shekara.

Jammiyyar mulki ta Democracy and progress Party wadda ake kira CDP a takaice ta zartar da sake gabatar shugaban kasar a matsayin dan takara a zabe mai zuwa ne a wani taron data gudanar na kasa wanda ya dauki yini biyu yana gudana a birnin Ouagadougou.

Zaben wanda zai gudana ranar 13 ga watan Nuwamba zai kasance karo na uku da jammiyar mulkin kasar ke tsayar da shugaba Blaise Campore,mutumin daya dauki shekaru 18 yana shugabancin Burkino faso.

Shugaba Compore dai ya haye ragamar mulkin wannan kasa data samu yancin kai daga faransa a shekarata 1960 ne tun daya kifar da gwamnatin wancan lokaci a shekarat 1987,an gudanar da zabe a kasar inda ya samu nasara a shekarata 1991,kana ya sake zarcewa kan mukamin nasa a zaben daya gudana a shekara ta 1998.

A watan oktoban bara nedai gwamnatin shugaba Compore ta sanar da gano yunkurin kifar da shi daga wannan mukami.A dangane da hakane aka cafke jamian soji 14 dana fararen hula 2,wadanda yanzu haka ke tsare domin gurfanar dasu gaban kotun musamman ta soji.

Wannan batu dai ya dada haifar da baraka tsakanin Burkino faso da Ivory Coast,a daidai lokacin da dangantakar kasashen biyu tayi tsami sakamakon zargin cewa ,ita Ivory Coast dake mawabtaka da ita ta kudanci, nada hannu cikin yunkurin juyin mulkin.

Akwai dai hasashen cewa shugaba Compare na Burkino faso yana da dangantaka ta kut da kut day an adawan Ivory coast wadanda sukayi yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Gbagbo a watan satumban shekarata 2002,batu daya tayar da rikicin da aka kasa warwarewa har yanzu a kasar ta Iviry coast,a hannu guda kuma ya raba kasar biyu.

A yayinda magoya bayan jammiyar dake mulki a wannan kasa suka amince da sake tsayar da shugaba Copoare a karo na uku a jere awannan kasa dake yammacin Afrika,jammiyyun adawa sun bayyana cewa hakan ya sabawa kundun tsarin mulki.

Bayan kifar da gwamnati a shekara ta 1987,da gudanar zabubbuka sau biyu da suka bashi nasara dai,shugaba Compore ya samu adawa daga jammiiyyun adawa,wadanda suka ki shiga wadannan zabe biyu a jere,saboda abunda suka bayyana da kasancewa rashin tsari da kuma magudi a bayyane.

A wata wasikar hadin gwiwa da suka yayata a ranar jummaar data gabata,jammiyun adawa 15 da ke kiran kansu Change 2005,na masu bayanin cewa shiga takaran shugaba Compore a zaben 13 ga watan nuwamba ya sabawa kundun tsarin mulkin ksa.

A shekara ta 2000 ne dai akayiwa kundun tsarin mulkin Burkino faso gyaran fuska ,inda aka rage tsawon lokacin da kowane shugaba zai iya kasancewa kan karaga daga shekaru bakwai zuwa shekaru biyar ,kana tazarce zai iya kasancewa sau daya ne kawai amma ba sabanin haka ba.

To sai dai jammiyar mulki ta bayyana cewa wannan sauyi bai shafi Campore ba,domin anyi gyaran ne lokacin da yake kan karaga a karo na biyu,don haka yanada dammar sake yin takara.

Burkino faso dai iatace kasa ta 175 daga cikin jerin kasashe 177 ,da mdd ta bayyana da kasancewa matalauta a duniya.Sama da kashi 80 daga cikin 100 na kimanin alummar kasar million 13 ke rayuwa kan kudi kasa da dalan Amurka 2 a kowane yini guda.